Jarumi a Masana’antar Kannywood, Tijjani Abdullahi Asase ya bayyana dangantakar da ke tsakaninsa da mawaki Dauda Kahutu Rarara a matsayin wacce ta wuce ydda wasu ke tsammani, domin kuwa a cewarsa ta wuce ta matsayin yaro da maigida, don kuwa yana yi wa Rarara kallon tamkar mahaifi a wajen nasa.
Tunda farko dai, Asase a wata hira da ya yi da RFI Hausa; ya bayyana irin yadda mutane, musamman mata da yara ke kallon sa a matsayin wani mutum mai ban tsoro sakamakon irin rawar da yake takawa a mafi yawancin fina-finansa; inda yake fitowa a matsayin dan daba.
- Alhaji Amadu Umar Ya Zama Sarkin Hausawan Garin Agbara A Jihar Ogun
- Muna Samun Nasarori A Yaki Da Gurbatattun Masana’antar Kannywood – Tijjani Asase
Ya yi nunu da cewa, wasu lokutan kuma abin yana ba shi mamaki ganin yadda wasu ke jin tsorosa idan ya zo waje; wanda a tunaninsa hakan bai rasa nasaba da irin rawar da yake takawa a fina-finai ba, in ji Asase.
Ya kara da cewa, kusan a duk fadin birnin Kano; babu wata unguwa da babu ‘yan daba a cikinta, hakan ya sa mafi yawancin matasa da aka haifa a can; za su iya kwaikwayar abin da ‘yan dabar ke yi, haka ni ma abin yake a wajena; domin kuwa ko ba a cikin fim ba, wasu lokutan nakan samu kaina a cikin irin wannan dabi’a idan aka bata min rai.
Don haka, wannan ba wani abu ne a wajena ba sabo; domin kuwa yadda nake a fim, ko kusa ba haka nake a gaske ba; domin duk wanda ya san rayuwata ta waje, zai yi shaidata a matsayin mutum mai son barkwanci da nishadi a kowane lokaci, in ji Tijjani Asase; wanda ya shafe shekaru fiye da 25 yana harkar fim.