Shugaban ma’aikatan fadar shugaban kasa, Farfesa Ibrahim Gambari ya ce ya zo jihar Kebbi ne domin isar da sakon sirri ga Gwamna Abubakar Atiku Bagudu da Sarkin Gwandu, Alhaji Muhammadu Iliyasu Bashar daga shugaban kasa Muhammadu Buhari.
Farfesa Ibrahim Gambari ya bayyana haka ne a lokacin da yake zantawa da manema labarai a gidan gwamnati a Birnin Kebbi, bayan ya dawo daga fadar sarki zuwa gidan gwamnati inda suka tattauna ta sirri da Gwamna Bagudu na kusan sa’a daya kafin tafiyar tasa.
Haka Kuma ya ce “Mai girma shugaban kasa ne ya aiko ni zuwa jihar Kebbi domin mu tattauna da Gwamna Abubakar Atiku Bagudu da Sarkin Gwandu Alhaji Muhammadu Iliyasu Bashar, shugaba Buhari na yin godiya da irin goyon baya da Kuma addu’arsu da suka bashi a wa’adin mulkinsa”.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp