Connect with us

RAHOTANNI

Na Iya Indiyanci Har Ina Shiri A Gidan Rediyo Saboda Sha’awar Harshen – Hafsat

Published

on

Sunana Hafsat Abdullahi Muhammad wadda aka fi sani da Hafsat Zeeaflam Priyanka

An haife ni agarin Kano unguwar Dorayi Chiranchi.

Na yi karatunan  firamare da sakandire a Kano, daga nan kuma na tafi makarantar gaba da sakandire wato jami’a  inda na karanci koyon aikin jarida a Management da ke cikin garin Kano

Na taso inason Indiya wanda ta kai ake min lakabi da suna Hafsat Zeeaflam Priyanka.

sakamakon kaunar indiyanci da nake yi muka kafa kungiya mai girman gaske a Kano wato Dostana Hamesha.

Wanda yandu haka ina gabatar da shiri na Indiyanci a radiyon pyramid  da ke Kano mai suna Chakde India Kano.

Ina jin indiyanci daidai gwargwado. Na koyi Indiyanci ne sakamakon yawan kallon fina-finai da kuma yawan abokantaka da su kansu Indiyawan. Kuma nakan tambaye su abnin da ya shige min duhu saboda yaren su ne, wanda ni da su yandu mun dama ‘yan’uwa.

Asalin harshena  gaba da baya shi ne Fulatanci wajen mahaifi da mahaifiya.

A gaskiya abin da ya ba ni sha’awa na koyi Indiyanci shi ne na tashi ne tun a gidanmu muna son Indiya. Fim din Indiya na taso nag a ana kalla a gidanmu musamman mahaifiyata wadda nake alfahari da ita domin da taimakonta na zama haka. Tana kara karfafa min gwiwa a wannan harka tawa ta Indiya domin ita ma tana son indiya sosai,wanda har ta kai su kansu Indiyawan sukan zo har gida su gaishe ta. Ba na mantawa kuma dadin dada wa abin da yake burge ni da harshen shi ne yadda ake karya shi.

Ina son Indiya musamman yarensu da su kansu da kuma yadda suke shigarsu wnda duk wanda ya sanni zai ganni cikin kayan Indiya kuma ina son rawarsu ma don komai na Indiya ba a bar ni a baya ba  hatta abincinsu ina iya dafa wa da kuma ci.

Wanda har takai ba ni da wasu aminai ko kawaye sama da su dama wadanda suke nan da kuma can.

Wanda da wasu ‘yan lokuta kadan akwai wani albishir da zan ba wa mutane game da Indiya a kan ci gabanmu mu masoya Indiya da kuma su kansu domin mun zama daya, wato kam gaskiya suna jin dadin yadda ‘yan Nijeriya suke kokarin wajen jin yarensu da al’adunsu,

Suna jin dadi matuka wanda haka ta sa ka zama nasu ku kulla alaka da su mai kyau wanda ka gani wadanda suke nan kasar tamu daidaiku ne wadanda ban san su ba

Saboda ina jin yarensu kuma inayin rawar ta Indiayan da saka kaya da abincinsu duk na iya

Suna jin dadi sun dauke ni kamar ta su, ko wane abu za su yi suna daukar shawara a guna ko ma mu yi abubuwa tare wanda yanzuma mun kulla kasuwanci da ni da su a halin yandu

gaskiya ban taba neman tafiya Indiya ba, sakamakon lokacin ina  ina karatu kuma sunaso naje amman naki saboda kada karatuna yasami gibi, amman yandu nagama karatuna kuma inatama shirye shiryen tafiya  halin yandu saboda sun inbiting dina tunda yandu akwai time na kammala karatuna dan tafi kuma suna ta farin ciki zan do saboda burinsu ke nan a kaina insha’ Allah zan je  kwanan nan,gaskiya abin da dance ga mutane shi ne idan dakai hulda da mutum ka yi tsakaninka da Allah tabbas dai taimakeka kuma duk wata kabila dakasani akwai nagari akwai mugu amman kullum fatanmu Allah ya hada mu dana kirki kuma ka da wai mutane su tsorata kawai mu sa Allah zai taimake mu, domin ni gaskiya duk wadanda nake tare da su banga wani wai mai mugun haliba a cikin kuma suna da matukar yawa wallahi duk da kowa da halinsa ammamn fatana nagari yandu in ka duba ako ina kasashen duniya ka ji an ce an kashe wani an yanke wani abu a jikinsa da sauransu shin su ba su da irin haka ne sai Indiya

Na farko za ni diyara da gudanar dawasu abubuw wanda su kansu Indiyan ne suka nemi tafiyar tawa saboda wasu business da za mu yi da su wanda muke son hada kan indiya da ‘yan Nijeriya domin a sami kyakkyawar alaka mai karfi tsakanin Indiya da Nijeriya.

tarbiya kome bangane rubutunba yimin bayani kasan hausar sai a hankali

agaskiya a kungiyarmu ta dostana hamesha akwai aji na koyar da yaren indiyanci wanda malamai suke gudanarwa irinsu auwal  dasauran malamai, wanda dayawa matasa sunata duwa kungiyarmu ta indiya wato dostana hamesha domin koyan yaren dakuma yin rawa ta indiya wanda kuma ibrhm yke yarda rawarbdasauran masubkoyarwa

kwanda har takai ake kiranmu duk wani show na indiya ana gayyatar mumuje

domin nisha dantar da mutane kuma dakaga kayan indiya mukesawa muyi ado kamar a indiya

hakane gaskiya kam zakaga a yandu dai duk mutanen dasu son indiya musamman a jahar kano gaskiya dakaga duk maison indiya soyayyarsa tafita daban da wanda baya sha awar indiya

kuma gaskiya abangaren soyayyya kam zan iya bude aji kuma sukansu indiyawa suna son muyi soyayya dasu wanda dayawa wasu sunmin tayin na auresu akwai musulmi da wadanda ba musulmaiba amman wadanda ba musulmai in fada musu cewar sadai sumusulunta saboda ni gaskiya son indiya badai candamin halayyata ta musulunciba kullum ina fifita musuluncina fiye da komai

kuma gaskiya ni a halin yandu bana soyayya saboda nafiso namaida hankali akan abinda nasa gaba duk da gaskiya babu abinda nafiso sama da soyayya amman ta gaskiya

amman ni ina tsoron soyayya da bahaushe saboda saikaga wani yanasonka yana kuma kula wata daban wanda ni atunanina wahalane da raba hankali amman indiya indai sukace suna sonka badasu iya kulawataba sabod zasuga kamar sunyi sabo sunada riko da amana akan soyayya sai kaga mutuwace ke iya rabasu da soyayya duk wuya duk runtsi sunatare basa duba wani yanada wani kawai sunada duba so amman mutanenmu na nan saikaga a idan kanason mace da anfara gulma karabu da ita to daman son bana gaskiyabane sukwa Indiya aiko ita ce tafi kowa tambari dasu aureta su son suke dubawa kuma su dauna lafiya

sakona ga mutanenmu na indiya na wato masu son Indiya shi ne mukara dagewa dan Allah akan yarennan kuma mucire tsoro ko fargaba akan duk wanda damu dauna dashi musa Allah daimana maganin komai

saikuma sako na abokanaina na can indiya main ara hi ho indiya insha Allah aur meri fans

Masoyana da wannan nake cewa kabhi albidana kehna Allah hafeez.

 
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: