Bayan yamutsin da ya kaure tsakanin masu zanga-zangar cewa, “Buhari ya dawo ko ya sauka daga mulki in ba zai iya ba.” karkashin jagorancin mawakin nan da aka fi sani da Charley Boy da masu goyon bayan shugaba Buhari a kasuwar Wuse dake Abuja.
Charly Boy, a jiya Laraba ya bayyanawa manema labarai a Abuje cewa, ya janye zanga-zangar da ya ke jagoranta mai taken “OurMumuDonDo” amma a saurari matakin da za su dauka nan gaba.