Daga Shehu Yahaya,
Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bayyana cewa ya kasa gane gidansa a Kaduna saboda irin ayyukan raya birnin da Gwamna Malam Nasiru el-Rufai ya yi. Shugaban kasan ya bayyana hakan ne lokacin da yake kaddamar da ayyukan da gwamnatin Jihar Kaduna ta samar. Buhari ya ce “Da nazo Kaduna ban gane gidana ba saboda ayyukan da Gwamna el-Rufai ke ta faman yi na gina kasa.”
Shugaba Buhari ya kara da cewa ” Na kasa gane ina ne gabas ina ne yamma domin Gwamna el-Rufai ya sauyawa Kaduna fasali da ayyuka. Shugaban kasar ya ce Jihar Kaduna tana ta koma tamkar wata kasa bisa irin shamfida ayyukan ci gaba daga Gwamnatin el-Rufai ya yi.
Buhari ya yi wannan kalaman ne lokacin da ya wuce ta kan titin Sultan da ke kusa da gidansa, titin na daya daga cikin titunan da Gwamnatin Kaduna ta mayar irin na zama. Shugaba Buhari ya kawo ziyarar aiki na kwana biyu a Jihar Kaduna domin kaddamar da ayyukan da gwamnatin jihar ta yi a cikin garin Kaduna da Zariya da kuma Kafachan.
Sai dai ziyarar ta shugaba Buhari ba ta yi wa wasu mazauna cikin garin dadi ba musamman na hana su fita domin neman na cefane. Duk manyan hanyoyin da suke cikin garin Kaduna a cike suke da jami’an tsaro wadanda suka hana jama’a zirga-zirga. Shugaba Buhari ya shago cikin garin Kaduna a ranar Laraba da misalin karfe bakawai na dare, amma bai hana wasu matasa yi masa ihu ba, inda suke cewa “Bamayi!
Bamayi!!. Rohotannai daga fadar gwamnatin Jihar Kaduna sun ruwaito cewa Shugaba Buhari ya ziyarci garin Zariya da Kafachan domin kaddamar da irin ayyukan da ya kaddamar a cikin Kaduna. A zantawarsu da wakilinmu, wasu al’ummar Jihar Kaduna sun ce ba sa murna da zuwan shugaban kasar sakamakon yadda gwamnatinsa ba ta kawo musu komai ba na ci gaba.
Malam Muhammadu Abdullahi, magidanci ne ya ce “Wai yanzu murnai me za mu yi da zuwan Buhari? muna cikin halin kunci na talauci da fargaban tsaro, to ta ina za mu yi murna da zuwansa” Nasiru Lawal, dan kasuwane a kasuwan Sheikh Abubakar gumi, ya ce “Yanzu maganar da muke yi, za ka shago kasuwa ka tarar kowa ya koma gida saboda zuwan shugaban kasa bude wasu ayyuka, saboda haka ‘yan kasuwa ba sa murna da zuwan Buhari Kaduna.
“Abu na biyu kuma, duk abubuwan da Gwamnatin Kaduna take yi na jefa al’umma cikin kuncin rayuwa Buhari yana sane, amma dai-dai da rana daya bai taba yin magana ba. Maganar gaskiya ba ma murna da farin cikin ziyarar shugaban kasa.” A shekarun baya al’ummar Jihar Kaduna suna yi wa Buhari tarba cikin jin dadi da farin ciki, amma wannan lokaci kowa na cikin bakin ciki wanda hakan baya rasa nasara da halin kuncin rayuwa da suka samu kansu a ciki, musamman ‘yan kasuwa wadanda gwamnatin Kaduna ya rusa wuraren kasuwancinsu.