Connect with us

JAKAR MAGORI

Na Samu Ciki Ba A Taba Jima’i Da Ni Ba – Wata Budurwa

Published

on

Wani bidiyo da ke yawo a kafofin sada zumuntar zamani na Florence Wathoni Anyansi, daya daga cikin masu shirin gidan BBNaija na wannan shekarar  ya bai wa jama’a da yawa mamaki.

Budurwar ta bayyana yadda ta samu juna biyu duk da kuwa da budurcinta kuma ba ta taba lalata da kowa ba a lokacin da ta ke shekaru 23. A bidiyon da a halin yanzu ya karade kafofin sada zumuntar zamani, mahaifiyar yaro dayan ta bayyana cewa ta samu dan wani lokaci tare da saurayinta su na shafe-shafen juna.

Daga nan ne ya goga mazakutarsa a gabanta har ya biya bukatarsa ba tare da ya shiga ko’ina ba. Wathoni ta ce bayan aukuwar lamarin ta daina ganin al’adarta, amma ba ta dauki al’amarin da muhimmanci ba saboda ta san ba zai yiwu ta samu ciki ba bayan basu yi wani abin a zo a gani ba.

‘Yar shekaru 29 a halin yanzu, ta bayyana cewa ta gano tana dauke da juna biyu ne bayan watanni biyar da aukuwar lamarin sakamakon gwaje-gwajen da ta yi.

“Har a lokacin da budurcina. A wannan ranar da muka yi soyayya da saurayina, ban taba tsammanin zan ga ciki ba saboda babu wani babban abu da ya shiga tsakaninmu. “Saurayin nawa babu abinda ya fi so da ya wuce ganin al’aurar mace. Ni kuwa na bar shi ya goga min mazakutarsa a gabana har ya fitar da maniyyi.

A haka na samu ciki,” a cewarta. “Bayan watanni biyar, na gano ina dauke da juna biyu. A lokacin nake tambayar kaina ta yaya hakan ta faru? “Na gano hakan ne a wata safiyar Lahadi bayan da na ziyarci wani mai sayar da magani. Ya bani abun gwajin ciki inda na tabbatar da cewa ciki gareni,” ta kara da cewa. Wathoni ta tuna yadda ta dinga fama da wahala wurin haihuwa saboda a budurwa take har lokacin.

A yayin martani ga wannan ikirarin, Folashade Olugbemi, wata likita wacce ta yi bayani a kai, ta ce hakan na iya faruwa a kimiyyance. Ta bayyana cewa ko da namiji bai sadu da mace ba, matukar ya zuba maniyyi a gabanta, akwai yiwuwar ya karasa ciki da kansa. “Hakan na iya faruwa. Kamar yadda ta ce, akwai yiwuwar cewa a wannan lokacin akwai kwai a cikin ta. A gaskiya maza basu bukatar maniyyi mai tarin yawa wurin yi wa mace ciki,” a cewar Olugbemi.

 
Advertisement

labarai