Na Shirya Kalubalantar Barcelona A Kotu – Neymar

Neymar

Daga Abba Ibrahim Wada

Dan wasan kungiyar kwallon kafa ta Paris Saint German kuma na tawagar kasar Brazil, Neymar, ya bayyana cewa ya shirya kalubalantar kungiyar Barcelona a gaban kotu bayan da tsohuwar kungiyar tasa ta bayyana cewa zata kaishi kotu akan ya karbi albashi a kungiyar sama da yadda yakamata ya karba.

A satin daya gabata ne Barcelona tace zata gurfanar da tsohon dan wasanta Neymar a gaban kotu saboda abinda ta kira biyan sa kudaden da suka wuce kima da suka kai Dala miliyan 12 lokacin da yake bugawa kungiyar wasa.

Jaridar El Mundo da ake wallafawa a kasar ta Sipaniya ta ruwaito cewar Neymar da yayi wasa a kungiyar Barcelona tsakanin shekarar 2013 zuwa 2017 ya karbi kudaden da suka wuce kima daga kungiyar a matsayin albashi.

Rahotanni sun ce dan wasan na Brazil na daga cikin sahun farko na ‘yan wasan da suka kaucewa biyan haraji a Spain, inda ake bin sa bashin sama da yuro 34 da rabi wanda hakan tasa har hukumomin kasar suka gurfanar dashi a gaban kotu.

Hukumomin Spain na kuma gudanar da bincike kan lokacin da Neymar yaje Barcelona da kuma tafiyar sa PSG sannan wata Kotu a Spain ta bukaci Neymar da ya biya Barcelona yuro miliyan 6 da dubu 790,000.

“Ban san abinda yake faruwa sai dai kawai in karanta a jarida kuma naga rahoton cewa zasu kaini kotu akan sun biyani kudade saboda haka ina mai sanar dasu cewar a shirye nake dana kalubalanci ikirarinsu a gaban kotu” in ji Neymar

Ya cigaba da cewa “Duk irin zargin da sukeyi inada hujjar d azan iya kare kaina saboda abune mukayi a rubuce cikin yarjejeniya da wakilaina su ma kuma a matsayinsu na kungiya da nasu wakilan babu wanda a ka yi wani abu a tsakaninmu ba tare daya amince ba”

A shekarun da suka gabata dai Barcelona taso ta sake sayan dan wasan daga PSG sai dai daga baya cinikin bai kasance ba sakamakon kudin da PSG ta bukata Barcelona ba zata iya biya ba kuma tun kafin bullar cutar Korona ma.

 

Exit mobile version