Hon. Alhassan Doguwa, ɗan majalisar tarayya daga Jihar Kano, ya yi alƙawarin nasarar jam’iyyar APC a Jihar Kano a zaɓen 2027.
Doguwa ya bayyana hakan ne a Abuja yau Lahadi yayin da yake maida martani ga wani iƙirarin da wani ɗan majalisar Kano, Hon. Abdulmumini Jibrin, ya yi, inda ya ce Doguwa ba zai iya taimaka wa APC ta samu nasara a Kano ba.
- PDP Ta Shafta Karya, Ba Mu Da Wata Alaƙa Da APC – KESIEC
- PDP Ta Shafta Karya, Ba Mu Da Wata Alaƙa Da APC – KESIEC
Doguwa, wanda yake wakiltar mazaɓar Tudun-Wada/Doguwa kuma shi ne shugaban kwamitin Majalisar wakilai kan albarkatun man fetur, ya ƙaryata zargin Hon. Jibrin. Ya bayyana kansa a matsayin jarumi da APC ke alfahari da shi a Jihar Kano da ma ƙasa baki ɗaya. Haka kuma, ya nuna sha’awarsa ta zama Darakta-Janar na kamfen ɗin APC a Kano a zaɓen 2027.
Mayar wa da juna magana tsakanin waɗannan ‘yan majalisar guda biyu ya daɗe yana faruwa, inda Jibrin, wanda yake wakiltar mazabar Kiru/Bebeji a ƙarƙashin jam’iyyar NNPP, ya zargi Doguwa da zama cikas ga zaman lafiya a Jihar Kano.