Shugaban majalisar wakilai, Femi Gbajabiamila, ya bayyana nadamar jagorantar taron da aka yi na tabbatar da Aminu Tambuwal a matsayin shugaban majalisar wakilai ta 7.
Aminu Tambuwal shine gwamnan jihar Sokoto mai barin gado kuma tsohon kakakin majalisar wakilai.
Da yake magana a Abuja a taron hadin guiwa – Majalisar 10 (Wakilai da Sanatoci), gamayyar mambobin jam’iyyar APC da jam’iyyun adawa a majalisar dokoki ta 10 mai zuwa a ranar Laraba, Gbajabiamila ya ce “na yi nadamar hakan,” – taimakawa Aminu waziri Tambuwal zama shugaban majalisar wakilai ta 7.
Gamayyar dai ta amince da ’yan takarar jam’iyyar APC a shugabancin majalisar wakilai, Tajudeen Abbas da Benjamin Kalu, a majalisar wakilai ta 10.
Kafin Gbajabiamila ya yi magana, dan takarar shugaban majalisar dattawa na jam’iyyar APC, Sanata Godswill Akpabio, shi ma ya halarci taron inda ya yi wani takaitaccen jawabi sannan ya fice.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp