Tsohon Gwamnan Jihar Kaduna, Malam Nasir El-Rufai, ya bayyana marigayi tsohon Shugaban Ƙasa, Muhammadu Buhari, a matsayin jagoran siyasarsa, wanda ya ƙarfafa masa guiwa har ya tsaya takarar gwamnan Kaduna.
A sakon ta’aziyyarsa, El-Rufai ya ce Buhari ya tsaya tsayin daka don ci gaban Nijeriya, ya bayar da gudummawa mai tsoka a matsayinsa na soja kuma shugaban ƙasa na mulkin soja da kuma zaɓaɓɓen shugaban ƙasa.
- Rasuwar Buhari: Na Yi Rashin Ɗan’uwa, Aboki, Ɗan Ƙasa Nagari —Babangida
- Rasuwar Buhari Babbar Asara Ce Ga Nijeriya — Obasanjo
El-Rufai ya ce Buhari ya kasance jarumi mai juriya wanda duk da tsige shi daga mulki a 1985, ya dawo kuma ya lashe zaɓe a 2015.
“Ko da yake bai cika magana ba, yana da natsuwa da barkwanci. Yana da hali mai sauƙi da ya sa talakawa ke ƙaunarsa, saboda suna ganin shi mutum ne mai gaskiya da amana.”
“Ko bayan faɗuwarsa a zaɓen shugaban ƙasa sau uku, ya sake tashi suka kafa jam’iyyar APC a 2013, wanda ya kayar da shugaban ƙasa mai ci a 2015. Ya kuma miƙa mulki cikin nasara a 2023, wanda hakan ya kafa tarihi.”
Ya ƙara da cewa ya samu damar yin aiki da Buhari a jam’iyyar CPC bayan zaɓen 2011, inda Buhari ya sa shi ya jagoranci kwamitin farfado da jam’iyyar. Kwamitin ne ya ba da shawarar haɗakar CPC da ACN da sauran jam’iyyu don tunkarar zaɓen 2015.
“Shugaba Buhari shi ne jagoran siyasa ta. Shi ya karfafa min guiwa na tsaya takarar gwamnan Kaduna. Ya halarci ƙaddamar da kamfe ɗina a watan Nuwamba 2014, kuma ya tsaya min har na kai ga nasara. Ina godiya sosai da goyon bayansa a lokacin gwamnatina, har da damar da na samu na tattaunawa da shi a kowane lokaci, ko da kuwa muna da saɓani a wasu manufofi.”
El-Rufai ya roƙi Allah Ya gafarta wa Buhari, Ya sanya shi a Aljannatul Firdaus, tare da bai wa iyalansa, musamman Hajiya Aisha Buhari da ’ya’yansa, hakurin rashinsa.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp