Tsohon ministan matasa da harkokin wasannin, Solomon Dalung ya ce yayi da ya sanin aiki da gwamnatin Buhari.
Dalung ya sanar da hakan ne a wata hira ta musamman da Freedom Radio.
“Matsalar tsaro a yanzun ta tilasta wa al’umma da dama a yankin Arewa sun bar muhallansu, wasun koma kwana a dazuka”. Inji Dalung
Dalung ya kuma zargi yadda gwamnatin Buhari ke almundahana da dukiyar al’umma da sunan samar da ayyukan raya kasa.
Tsohon Ministan ya kara da cewa, ayyuka da dama da gwamnati mai ci ta gada ta gaza karasa su, duk da makudan kudaden da ake fitarwa domin kammala su.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp