NAF Ta Fatattaki ’Yan Bindiga Da Kashe Mayakansu A Kaduna

Kaduna

Daliban sojojin sama na rukunin 4/2019 su na gwada yadda a ke sarrafa babbar bindiga a lokacin bikin yaye su.

Daga Mahdi M. Muhammad,

Rundunar sojojin saman Nijeriya (NAF), bagaren dakarun ‘Operation Thunder Strike’ sun yi nasarar kashe wasu ‘yan bindiga masu yawa a dajin Chikwale da ke yankin Mangoro na karamar hukumar Chikun ta jihar Kaduna.

Jami’in yada labarai na hedikwatar tsaro, Manjo Janar John Enenche ne bayyana haka a cikin wata sanarwa da ya sanya wa hannu cikin makon nan, a inda yake cewa, an gudanar da aikin ne a ranar, 23 ga watan Janairun, 2021, biyo bayan rahotannin sirri na sahihanci da ke nuna yawan ‘yan bindiga a yankin, wanda yake kusan kolimita 20 da babbar hanyar Kaduna zuwa Abuja.

Dangane da haka ne, bayan jerin samfuran tsaro na sama, rundunar ta aika da wata rundunar da ta dace da jiragen saman yaki masu saukar ungulu don kai hari wurin.

Sama da yankin da aka nufa, jirgin ‘NAF Intelligence, Surbeillance and Reconnaissance (ISR)’ ya hangi wasu ‘yan bindiga a kan babura sanye da bakaken kaya sun nufi jihar Neja. Saboda haka jirgin ya yi ta bi-ta-da-kai tare da shiga yankin da ‘yan bindigar suke, wadanda aka ga suna kokarin bude wa jirgin wuta yayin da yayo kansu.

Exit mobile version