Huklumar NAFDAC ta ja kunnen ‘yan Nijkeriya cewar su yi hankali wajen amfani da ko kuma, lokacin da suke sayen fatar dabbobi, wadda aka fi siani da ‘ponmo.’
Babban darektan Hukumar Moji Adeyeye ta bayyana cewar dab akwai wadansu ‘yan kasuwa wadanda su kuma ba wani abinda ya dame su, illah su samu kudade kota halin kaka,: “Wadanda yanzu suke yin wata hanya da fatar data kamata masana’ntu suyi amfani da ita, wajen amfanin da ake da ita wajen ci.”
Mrs Adeyeye ta bayyana cewar binciken da aka gudanar ya bayyana cewar da akwai wadansu kamfanoni, wadanda suke shigo da Fatu daga wasu kasashe kamar su Lebanon da kumna Turkiyya.
Ita dai sanarwar ta kara da cewar amfani ko kuma cin fatun wadannan namun dajin, hakann yana iya sa mutum ya kamu da cutar Hanta, Koda, da kuma matsalar data shafi Zuciya, da akuma akwai yiyuwar kamuwa da Aplastic anaemia, sai kuma matsalkar jijiyar da take tsakiyar jikin mutum, wasu abubuwan da ka iya cutar da mutum , da kuma cutar Kansa.