Shugaban hukumar nan da ke sanya idanu kan man da ake hakowa a kan tudu, Gbenga Komolafe, ya ce Nijeriya ta tafka asarar akalla naira biliyan 434 saboda satar da ake yi na mai tsakanin watan Janairu zuwa watan Maris na wannan shekarar ta 2022.
BBC ta rawaito cewa, nn tafka wannan asara ce adaidai lokacin da karaminin Ministan man fetur, Mista Timipre Sylva, ke cewa kamfanonin mai masu zaman kansu a Nijeriya na barin kasar saboda hadarin da suke fuskanta.
Shi ma, attajirin Afirkan nan kuma shugaban rukunni kamfanin Dangote, Alhaji Aliko Dangote ya shawarci gwamnatin Nijeriya ta fito da tsarin bai-daya kan kudaden haraji domin karfafawa masu zuba jari a fanin hako mai ta tudu da kuma cikin teku.
Komolafe ya ce an iya fitar da gangan miliyan 1.35 ko kashi 71 cikin 100 na gangan miliyan 1.9 da ake samarwa, saboda satar da ake fuskanta da farfasa batutan mai.
Ya kuma jadada cewa wannan na daga cikin matsalolin da ke sake kassara Nijeriya.