Hajiiya Naja’atu Bala Mohammed, wadda aka fi kiranta da Hajia Naja musamman a tsakanin ‘yan gwagwarmaya da ‘yan siyasa a fadin tarayyar Nijeriya. Ta yi fice a fagen a fafutkar kare hakkin mata da al’umam gaba daya a fadin Nijeriya.
Ita ce kuma mace ta farko da ta lashe zaben kujerar majalisar dattawa mai wakiltar mazabar Kano ta tsakiya, haka kuma ita be mace ta farko da ta zama shugabar kungiyar daliban Jami’ar Ahmadu Bello da ke Zariya a zangon karatu na shekarar 1982/83.
- Tsare-tsaren CBN Don Samar Da Kyakkyawar Alkibla Ga Tattalin Arzikin Nijeriya
- ‘Yan Bindiga Kamar Dabbobi Suke, Mun Samu Makamin Da Zai Datsa Su Biyu —Matawalle
An haifi Hajiya Naja’atu Bala Muhammad ne a shekarar 1956 a garin Kanon Dabo, mahaifinta Alhaji Ali Abdullahi, ciakknen dan Jami’yyar NEPU ne da ya yi zamani da Malam Aminu Kano.
Ta yi karatu a makarantar ‘St. Louis Pribate School’ Kano, ta kuma yi karatun koyon aikin malanta a ‘Women’s Teachers’ College’ kafin ta zarce zuwa Jami’ar Ahmadu Bello Zariya inda ta samu kammala karatu a fannin digiri a tarihi.
Naja’atu Bala Mohammed ta auri marigayi Dakta Bala Mohammed wanda shi ne mai ba Marigayi Gwamnan Jihar Kano Alhaji Abubakar Rimi, shawara a kan bangaren harkokin siyasa.
A ranar 10 ga watan Yuli 1981 wasu gungun masu tarzoma suka kashe shi, kafin rasuwarsa mutum ne da ya yi Imani da akidun siyasar Jam’iyyar PRP na Marigayi Aminu Kano.
Naja’tu Bala Mohammed ta bayyana baiwa da Allah ya bata na shbugabanci tunlokacin da ta shiga harkar siysaa a jami’a ta kuma samu nasarar tafiyar da harkokin dalibai yadda ya kamata a wannan lokacin.
Tabbas ta kafa tarihi na zama shugabar kungiyar daliban jami’ar ABU ta kuma zama mataimakiyar shugabar kungiyar dalibai na kasa wato NANS.
Shighar Naja’atu Bala Mohammed harkokin siyaasa ya taimaka wajen zaburar da matan arewacin Nijeriya inda aka kai ga samun mata da ma sun shiga don a dama da su a harkar gudanar da mulkin al’umma.
Ta rike mukamai da dama da suka hada na shiga tsakani don sasanta rikicin ‘yan Boko Haram da gwamnatin tarayya, ba ta taba ganin aikinta cikin maza wani abu ne da zai hana bayar da nata gundummawar ba, tana daukar haka a matsayin sama ce na ta bayar da na gudumawar don daukaka kasarta Nijeriya, musamman abin da ya shafi tabbatar da zaman lafiya.
A wasu lokutta ta ki karbar wasu nadin da aka yi mata na mukamai, musanmman nadin da aka yi mata na zama ‘yar kwamitin gudanarwar Jam’iar Gwamnatin Tarayya da ke Dutse, inda ta ce ba a kai ga tuntubarta ba kafin a yi mata nadin. A halin yanzu ta karbi mukamin kwamishiniya a hukumar kula da aikin.