Abdulrazaq Yahuza Jere">
Leadership Hausa Newspapers
No Result
View All Result
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
No Result
View All Result
Leadership Hausa Newspapers
No Result
View All Result
Home

Namijin Kokarin NIS A Bisa Aiki Da Kundin Kula Da Iyakokin Kasa Na 2019-2023

by Abdulrazaq Yahuza Jere
January 3, 2021
in LABARAI
4 min read
Namijin Kokarin NIS A Bisa Aiki Da Kundin Kula Da Iyakokin Kasa Na 2019-2023

Shugaban NIS CGI Muhammad Babandede MFR (a hagu), Ministan cikin gida Rauf Ogbeni Aregbesola da wani jami'i yayin da aka kaddamar da Kundin Kula da Iyakoki na 2019-2023, a watan Agustan 2019.

WhatsAppShare on FacebookShare on TwitterShare on Telegram

Hukumar Kula da Shige da Fice ta Kasa (NIS) wacce aka dora wa nauyin kula da shige da ficen kasa da tsaron iyaka, ta himmatu wajen jagorantar yaki da kai-komon bakin-haure ta hanyar amfani da tsararren kundin kula da iyakoki na 2019 zuwa 2023.

Shi dai wannan kundi an samar da shi ne da nufin dakile safarar bil’adama, fasa-kwaurin bakin-haure da kuma daukar wasu matakai na hana tuttudowar ‘yan gudun hijira na Nijeriya da ke barin gidajensu sakamakon ta’addanci, da barnar ‘yan bindiga da rikicin gonakai zuwa kasashe makota irin su Nijer, Chadi da Kamaru.

samndaads

Domin ganin haka ta cimma ruwa, NIS a karkashin shugabancin CGI Muhammad Babandede MFR ta sake yin kyakkyawan tsari na aiki inda ta aike da jami’anta da suka samu horo na musamman domin kula da iyakokin kasa. An samar da sansanoni na musamman ga wadannan kwararrun jami’ai a sassa 14 na kasar nan da suke bakin iyakoki masu fama da ta’addancin ‘yan bindiga a arewa maso gabas, da arewa maso yamma da arewa maso tsakiya. Sansanonin da aka samar a Mazanya da ke shiyyar Jibiya da Daura a Jihar Katsina su ne ke kula da wasu sassa na arewa maso gabas da arewa maso yamma. An samar wa jami’an da ke aiki a wadannan sansanoni kayan aiki na zamani da suke daukar hoto da bidiyo tare da aikewa da su kai-tsaye zuwa babbar cibiyar aiki da ke shalkwatar hukumar a Abuja domin mahukuntan da suka dace su duba da kuma tantancewa.

Tun a shekarar 2009, NIS ta rika kasancewa a kan gaba domin bayar da gudunmawa a yankin arewa maso gabas inda jami’anta suke aiki a rundunar hadin gwiwa a karkashin ayyukan tsaro na musamman da sojoji ke yi na Operation Lafiya Dole da sauran wasu daban-daban da ake yi a fadin kasar nan ciki har da atisayen kula da iyakoki a karkashin ofishin mai bai wa shugaban kasa shawara a kan tsaron kasa domin tabbatar da bin ka’ida wajen shige da ficen kasa. Har ila yau, jami’an hukumar sun yi aikin sanya ido a kan tsaro a lokutan zabuka daban-daban inda suka yi nasarar cafke wasu da ba ‘Yan Nijeriya ba suna kokarin kada kuri’a a garuruwan da ke kan iyaka.

Wadannan ayyuka sun kasance masu kalubale amma duk da haka hukumar ta yi aiki kan-jiki-kan-karfi wajen cimma muradun gwamnati da na mutanen da ake jigilarsu ana tsaka da yaki da cutar. NIS ta samar wa jami’anta da ke sahun gaba a bakin aiki da rigunan kariya daga Korona tare da gudanar da sauran aikace-aikace na gabar teku cikin kwarewa domin dakile haramtattun tafiye-tafiye ta ruwa.

NIS ta cafke mutane da dama a jihohin Kuros Riba da Akwa Ibom saboda kasancewar jihohin masu makotaka da Kamaru. Wadanda aka kama da laifi; ko dai an fatattake su sun juya inda suka fito ko hukunta su bisa doka. Ta kuma gurfanar da fasinjojin da aka kama da dama a cikin kananan kwale-kwale tare da tasa keyarsu zuwa gidajensu, sannan aka kwace kwale-kwalen aka mika wa ‘yan sanda. Bugu da kari, hukumar ta hukunta wasu tsirarun ‘yan kasashen waje da aka kama da laifuffukan da suka shafi fasfo na Nijeriya da wasu na kasashen ketare.

Tabbas, darussan da hukumar ta kara koya a wannan lokaci na mawuyacin hali sun kara taimaka wa shugabanta a kan lalubo hanyoyin aiki na zamani inda a kan haka aka samar da na’urorin tantance matafiya (MIDAS) a manyan filayen jiragen sama da manyan mashigan kasa domin tattara bayanai da saukaka ayyukan tantance fasinjoji.

Ba a wannan ne kawai NIS ta mayar da hankali ga zamanantar da ayyukanta ba, akwai gagarumin aikin da ta mayar da hankali a kai na samar da katafaren ginin fasahar zamani, inda za ta mayar da ayyukanta su rika gudana ta na’urorin da ake yayi na zamani kamar yadda ake yi a kasashen duniya da suka ci gaba. Tasoshin da aka samar na aiki da na’urorin zamani za su maye gurbin wadanda ake yi da hannu kawai wajen bayar da biza, fasfo, takardar izinin zama a kasa, bincike-bincike da kuma tattara bayanan sirri na hukumar. Dama dai tuni aka mayar neman takardar izinin aiki na wucin-gadi da biza-nan-take zuwa na’urar zamani. Cike takardar nema da biyan kudin abubuwan duk an mayar da su ta shafin intanet. An haramta biyan tsabar kudi tare da shawartar duk wani mai son biza ko fasfo ya garzaya shafin NIS na intanet ya gabatar da bukatarsa. Wannan ya taimaka gaya wajen hutar da kwastamomi da magance matsalar ka-ce-na-ce a tsakaninsu da jami’ai da kuma uwa-uba habaka aiwatar da kudirin gwamnati na saukaka hada-hadar kasuwanci a kasar nan.

Hakika, NIS a karkashin shugabancin CGI Muhammad Babandede MFR tana samun gagarumin sauyi ta hanyar zamanantarwa, wannan kuma ya kara wa hukumar tagomashi saboda nan da ‘yan shekaru kadan duk wata hukuma ko ma’aikata wajibi ne ta sabunta kanta zuwa zamani, in ko ba haka; za a bar ta tana cin tuwo da miyar bara. Shi ya sa NIS ta kara matsa kaimi wajen kakkafa na’urorin zamani wajen kula da iyakokin kasa a wani bangare na cimma kudirin da Babandede yake da shi mai taken “idan aka samu tsaron iyaka, cikin kasa zai samu ingantaccen tsaro”.

Bugu da kari, da yake an samu sake barkewar cutar Korona a karo na biyu, NIS ta yi tsayuwar daka wajen ganin ta bunkasa sassan ayyukanta da na’urorin aiki na zamani ta yadda za a rika biya wa abokan hulda bukatunsu ba tare da hulda a tsakanin mutum da mutum ba, sai fa idan ya zama wajibi abokan huldar su hallara kuru-kuru.

Haka nan, Jami’in hulda da jama na hukumar, DCI Sunday James ya bayyana cewa a yayin da NIS ke shirin fara aiki da katafaren gininta na fasahar zamani, hukumar tana karfafa gwiwar masu hulda da ita su ci gaba da amfani da shafinta na intanet, saboda babu wani tsabar kudi da za a amince da shi a sabon tsari aiki na hukumar.

SendShareTweetShare
Previous Post

Kaseem Sulaimani: Janar Din Da Ya Kawo Karshen ‘Yan Ta’addan ISIS

Next Post

Na’urar Bincike Ta Tianwen-1 Za Ta Sauka A Duniyar Mars Bana

RelatedPosts

NIS Ta Kaddamar Da Sansanin Karfafa Tsaron Iyakar Kasa Na 15 A Jihar Ogun

NIS Ta Kaddamar Da Sansanin Karfafa Tsaron Iyakar Kasa Na 15 A Jihar Ogun

by Abdulrazaq Yahuza Jere
11 mins ago
0

A kokarinta na tabbatar da tsaron iyakokin kasar nan, Hukumar...

Sakataren Lamurran Sirri Na Gwamnan Bauchi Ya Yi Murabus

Sakataren Lamurran Sirri Na Gwamnan Bauchi Ya Yi Murabus

by Abdulrazaq Yahuza Jere
3 hours ago
0

Daga Khalid Idris Doya Rahotonnin da suke fitowa daga fadar...

Tattabaru

Abin DaYa Sa Tattabarun Da Buhari Ya Saki Ba Su Tashi Ba – Adesina

by Abdulrazaq Yahuza Jere
4 hours ago
0

Daga Rabiu Ali Indabawa, Mashawarci na Musamman ga Shugaban Kasa...

Next Post
Tianwen-1

Na’urar Bincike Ta Tianwen-1 Za Ta Sauka A Duniyar Mars Bana

Domin sanya talla ko karin bayani a tuntube wannan numbar +2348126152609.

Leadership Epaper
ADVERTISEMENT
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
Advertise with us

© 2020 Leadership Group .

No Result
View All Result
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU

© 2020 Leadership Group .

Go to mobile version