Hukumar hana safarar mutane ta ƙasa (NAPTIP) ta kai sumame wani gidan haya da ake zargin gidan tara mata masu haihuwa ne a unguwar Ushafa da ke Abuja, inda ta ceto mata masu juna biyu har su tara.
Hukumar ta ce an kulle matan ne a gidan hayar da wani ɗan damfara ya kama, bayan ya ɗauke su aiki ta hanyar wani dandalin yanar gizo. Kakakin NAPTIP, Vincent Adekoga, ya ce an samu labarin gidan ne daga wani mai kishin al’umma.
- Yansanda Sun Kama Mutum 6 Bisa Zargin Satar Keke-napep Uku A Adamawa
- NAPTIP Ta Kuɓutar Da Yara 19 Da Aka Sace A Kebbi
A wani al’amari kuma, Kotun Babban Birnin Tarayya da ke Gudu ƙarƙashin Mai Shari’a Adebiyi Osolo ta yanke wa wani fasto mai suna Bishop Kenneth Duke hukuncin shekaru 20 a gidan yari ba tare da zaɓin biyan tara ba, bayan ta same shi da laifin yi wa wata yarinya ’yar shekara 12 fyaɗe.
Yarinyar, wacce mahaifiyarta ta ba da ita kula ga faston, ta gamu da wannan mummunan lamari ne a watan Maris 2023.
Shugabar NAPTIP, Binta Adamu Bello, ta yaba wa kotun bisa wannan hukunci, tana mai cewa zai zama izina ga wasu. Ta ce, “Fyaɗe laifi ne mai muni wanda ke haifar da mummunan tasiri a hankali da tunanin wanda aka yi wa shi. Dole ne mu haɗa kai don magance wannan aika-aika.” Ta kuma yi gargaɗi cewa hukumar ba za ta yi sassauci ga duk wanda aka samu da wannan laifi ba.