Wani binciken kuri’ar jin ra’ayoyin jama’a da aka gudanar a kasashe 22 dake nahiyoyi biyar ya nuna cewa, yawancin al’ummar kasashen duniya sun yaba da nasarorin da Sin ta samu a cikin shekaru 10 da suka gabata, inda kashi 78.34% na wadanda suka amsa wadannan tambayoyi a duniya sun yi imanin cewa, tattalin arzikin Sin ya zama injin din raya tattalin arzikin duniya, wanda ya kara kuzari da kwarin gwiwa ga tattalin arzikin duniya.
Cibiyar nazari ta kafar CGTN wadda ke karkashin babban rukunin gidan rediyo da talabijin na kasar Sin CMG da cibiyar nazarin yanayin yayata bayanai da harkokin mulkin kasa dake karkashin jami’ar Renmin ta kasar Sin ne suke fitar da rahoton mai taken “Sin a sabon zamani” cikin hadin gwiwa.
Wadanda suka amsa tambayoyin, sun hada da mazauna kasashe masu sukuni kamar Amurka da Ingila da Faransa da Jamus da Kanada da Australia da New Zealand da Japan da Koriya ta Kudu da Singapore da sauransu, da wasu kasashe masu tasowa kamar Brazil, Argentina da Mexico da Thailand da India da Pakistan da hadaddiyar daular Larabawa da Masar da Nijeriya da Kenya da Afirka ta Kudu da sauransu.
Sakamako ya nuna cewa, wadanda suka yaba da nasarorin da kasar Sin ta samu wajen raya tattalin arzikin Sin da suke zaune a Afirka ya kai kaso 91.46 cikin 100, yayin da Turai ke biyo mata baya a matsayi na biyu, da kashi 81.60%, Amurka ta Arewa ne ke matsayi na uku da kashi 78.09%. (Safiyah Ma)