ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Saturday, July 18, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Dalilin Da Ya Sa Aka Horar Da Manoman Tumatir 100 A Garin Zariya

by Abubakar Abba
2 hours ago
Manoman

Manoman Tumatir kimanin su 100 aka horar, kan sarrafawa da sayar da shi, tare kuma da rage yawan asarar da suke yi bayan noma shi.

Kazalika, an horar da su a kan yadda za su rika ba shi kariya daga dumamar yanayi.

Horon, wanda ya gudana a garin Zariya da ke Jihar Kaduna, shirin cibiyar gudanar da bincike ta Afirka (FAR-LeaF II), ta yi horon ta hanyar hadaka da cibiyar NSPRI ta kasa, da kuma cibiyar NIFAAS da sauran abokan hadaka.

ADVERTISEMENT

Shugabar taron a yawabinta a wajen horon, Dakta Ololade-Latifat Abdulrahman ta sanar da cewa; an kirkiro shirin ne, domin dakile barazanar dumamar yanayi da ke yi wa nomansa illa, tare da inganta rayuwar dubban ‘yan Nigeriya da suka dogara a kan amfanin gona.

Har ila yau, ta danganta Tumatari a matsayin wani abu mai matukar muhimmanci a abinci da samar da kudaden shiga ga masu nomansa da kuma samar da ayyukan yi, ga miliyoyin ‘yan kasa.

LABARAI MASU NASABA

Sharhi A Kan Dabarun Zamani Na Yin Auren Ƴaƴan Itatuwa

Me Ya Sa Har Yanzu Manoma A Arewa Suka Gwammace Yin Noma Da Galmar Shanu

Haka zalika, Dakta Ololade, ta sanar da cewa; karancin ruwan sama da sauyin yanayi da cututtukan da ke lalata shi da kuma yawan asarar da manomansa ke fuskanta, na jawo koma baya ga nomansa.

A cewar tata, wannan horo na da matukar muhimmanci, domin kuwa zai kara taimaka wa wadanda suka amfana da shi wajen kara yawan girbi mai yawan gaske da rage asara da samar da ayyukan yi da kuma samar da wadatarsa a daukacin fadin kasar.

Ta kara da cewa, horon na daga cikin aikin yakar dumanar yanayi na Tumatir wato, CBACTBCA, wanda ya yi duba a kan illar dumamar yanayi ga masu ruwa da tsaki a fannin na nomansa, tare da kara karfafa guiwar rungumar dabarun nomansa.

Ta ci gaba da cewa, bincike ya nuna cewa; akwai bukatar kara habaka samar da daukin da zai taimaka wa manomansa, masu sarrafa shi da sayar da shi da kuma yin safararsa, musamman domin su rungumi tsarin kaucewa dumamar yanayi da ke yi masa illa.

Bugu da kari, Dakta Ololade ta bayyana cewa; wadanda suka amfana da horon, za a raba musu ingantaccen Irin Tumatir da sauran kayan zamani na rage dumamar yanayi.

Ta kuma yaba wa shirin na FAR-LeaF II da Cibiyar NSPRI da NIFAAS da kuma sauran abokan hadaka, kan gudunmawar da suka bayar ga shirin.

Shi ma a nasa jawabin a wajen horon, wani manomi da ya amfana da horon, kuma  Malamin Aikin Gona daga Hukumar Bunkasa Aikin Gona ta Jihar Kaduna (KADA), Malam Aliyu Umar, ya sanar da cewa; ya amfana da horon, musamman kan yadda manoman Tumatirin, za su rage yin asara bayan sun yi girbi.

Ya ce, ingantaccen Irin na Tumatir da aka raba wa mahalarta horon, zai taimaka wa manoman, musamman wajen rage dumamar yanayi, yayin da suka shuka shi.

Wata manomiyar Tumatir, wadda ita ma ta amfana da horon, Malama Asibi Hassan, wacce ta fito daga Karamar Hukumar Sabon Gari da ke Jihar Kaduna ta sanar da cewa; horon ya zo a kan gaba, musamman duba da yadda mahalartansa suka samu ilimi kan yadda za su adana Tumatirin da suka girbe.

Ta kuma danganta tashin farashinsa a wasu sassan kasar, sakamakon karancin kayan aiki na zamani da na adana shi, inda ta sanar da cewa; akasarin Tumatirin da aka noma, na lalacewa a hanya ne kafin ya isa kasuwa.

Malama Asibi, ta kuma yi kira ga matakan gwamnati uku na kasar da sauran abokan hadaka a fannin na nomansa, da su taimaka wajen bai wa manomansa horo da samar musu da kayan aiki na zamani da sauran makamantansu.

Manoman
Abubakar Abba
+ postsBio
  • Abubakar Abba
    https://hausa.leadership.ng/author/abubakar-abba/
    Dalilin Da Ya Sa Kungiyar NCTR Ta Jinjina Wa Shugaban NPA
  • Abubakar Abba
    https://hausa.leadership.ng/author/abubakar-abba/
    Nazari A Kan Wasu Cututtuka Da Ke Shafar Dabbobi Lokacin Damina
  • Abubakar Abba
    https://hausa.leadership.ng/author/abubakar-abba/
    Sharhi A Kan Dabarun Zamani Na Yin Auren Ƴaƴan Itatuwa
  • Abubakar Abba
    https://hausa.leadership.ng/author/abubakar-abba/
    Ɗantsoho Ya Jinjina Wa Hukumar FCC Kan Sabbin Sauye-Sauyen Da Ta Samar

MASU ALAKA

Labarin Farfesoshi Tagwaye Da Suka Yi Karatun Digiri Tare Suna Aiki Tare A Wuri Ɗaya
Noma Da Kiwo

Sharhi A Kan Dabarun Zamani Na Yin Auren Ƴaƴan Itatuwa

July 11, 2026
Me Ya Sa Har Yanzu Manoma A Arewa Suka Gwammace Yin Noma Da Galmar Shanu
Noma Da Kiwo

Me Ya Sa Har Yanzu Manoma A Arewa Suka Gwammace Yin Noma Da Galmar Shanu

July 4, 2026
Dalilin Masu Kiwon Kajin Gidan Gona Na Sukar Haɗakar Gwamnatin Tarayya Da Chana
Noma Da Kiwo

Dalilin Masu Kiwon Kajin Gidan Gona Na Sukar Haɗakar Gwamnatin Tarayya Da Chana

July 3, 2026
Next Post
Tasirin Da VAR Ta Yi A Gasar Kofin Duniya

Tasirin Da VAR Ta Yi A Gasar Kofin Duniya

LABARAI MASU NASABA

An Kama Matashi A Kano Kan Zargin Kashe Abokinsa

‘Yansanda Sun Kama Mutum Biyu Kan Zargin Damfarar Wayar Salula A Jihar Adamawa

July 18, 2026
Sabon Tsarin Tikitin Abinci Na Nusuk Zai Iya Ƙara Kuɗin Bizar Umrah

Sabon Tsarin Tikitin Abinci Na Nusuk Zai Iya Ƙara Kuɗin Bizar Umrah

July 18, 2026
Tasirin Da VAR Ta Yi A Gasar Kofin Duniya

Tasirin Da VAR Ta Yi A Gasar Kofin Duniya

July 18, 2026
Dalilin Da Ya Sa Aka Horar Da Manoman Tumatir 100 A Garin Zariya

Dalilin Da Ya Sa Aka Horar Da Manoman Tumatir 100 A Garin Zariya

July 18, 2026
Sin Za Ta Inganta Kaddamar Da Aikin Kungiyar Hadin Gwiwar AI Ta Duniya Da Wuri

Sin Za Ta Inganta Kaddamar Da Aikin Kungiyar Hadin Gwiwar AI Ta Duniya Da Wuri

July 17, 2026
Tinubu Da Atiku Da Obi Na Ci Gaba Da Zafafa Neman Kuri’un Arewacin Nijeriya

Tinubu Da Atiku Da Obi Na Ci Gaba Da Zafafa Neman Kuri’un Arewacin Nijeriya

July 17, 2026
Sin Ta Yaba Da Matakin Amurka Na Kin Tsawaita Dokar Ta-Baci Dangane Da HK

Sin Ta Yaba Da Matakin Amurka Na Kin Tsawaita Dokar Ta-Baci Dangane Da HK

July 17, 2026
Zaben 2027:Tikitin Muslim-muslim Na Jam’iyyar APC Ya Sake Tayar Da Kura

Zaben 2027:Tikitin Muslim-muslim Na Jam’iyyar APC Ya Sake Tayar Da Kura

July 17, 2026
Xi Ya Gana Da Babban Sakataren MDD Da Firaministocin Thailand Da CambodiaA

Xi Ya Gana Da Babban Sakataren MDD Da Firaministocin Thailand Da CambodiaA

July 17, 2026
Zaben Fidda Gwani Da Ake Takaddama:APC Ta Dauki Matakan Kauce Wa Shari’o’in Kotu

Zaben Fidda Gwani Da Ake Takaddama:APC Ta Dauki Matakan Kauce Wa Shari’o’in Kotu

July 17, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.