Daga shekarar 1966 zuwa 2020, Nijeriya ta yi Ministocin Aikin Gona daidai har guda 52.
Sai dai, abin takaicin shi ne; bayan tsawon shekara 54, ba a samu wata gagarumar nasara ta a zo a gani ko wani sauyi ga wannan fanni na aikin noman a fadin wannan kasa ba.
- Gwamnatin Tarayya Za Ta Rage Kudin Sufuri Da Kashi 40 Ta Hanyar Amfani Da Motoci Masu Iskar Gas
- Ranar ‘Yanci: Jihar Kano Ta Zama Madubin Dubawa A Kan Kyakkyawan Shugabanci – Gwamna Abba
Har zuwa yanzu, wasu manoma a kasar nan; na ci gaba da amfani da Fatanya da sauran kayan noma na gargajiya.
Haka zalika, har zuwa yau; wasu manoma a wannan kasa na amfani da Galmar Shanu wajen yin noma, musamman a Arewacin Nijeriya; inda kuma wasu gonaki ‘yan kalilan na masu zuba hannun jari, na masu noma daga ketare; ke amfani da kayan aikin noma na zamani.
Wasu daga cikin fitattun tsoffin Ministocin Ma’aikatar Gona na wannan kasar, wadanda suka hada da Cif C.O. Komolafe, Otunba Bamidele Dada, Adamu waziri, Dakta Joe Okezie, Malam Adamu Ciroma, Cif Ola Awotesu, Farfesa Jerry Gana, Madam Ada Adogu, Marigayi Alhaji Abubakar H. Hashidu, Cif Chris Agbobu, Dakta Shettima Mustafa, Dakta Grace Ogwuche da kuma Dakta Malami Buwai.
Sauran su ne, Dakta Garba J.A Abdulkadir, Dakta Hassan Adamu. Alhaji Sani Zangon Daura, Dakta Sayyadi Abba Ruwa, Alhaji Dakta Fidellia Njeze, Isa Muhammed, Alhaji Bala Sakkwato, Alhaji Adamu Bello, Dakta Akinwumi Adesina, Cif Audu Ogbeh, Alhaji Sabo Nanono da kuma Mohammad Mahmood Abubakar Tanko.
Sai dai, wasu daga cikin wadannan tsoffin ministocin; kamar Jerry Gana da wasu daga cikinsu, ba su shekara guda a kan mukamin ba.
Tsohon Ministan Ma’aikatar, Alhaji Adamu Bello; shi ne wanda ya jima yana rike da mukamanin ministan ma’aikatar, inda ya shafe shekaru shida; a lokacin mulkin tsohon shugaban kasa, Cif Olusegun Obasanjo.
Duk da irin wadannan jiga-jigan manyan mutane da suka shugabancin ma’aikatar ta noma, fannin ya samu koma-baya.
Har ila yau, fannin ya samu koma bayan ne; sakamakon irin rikon sakainar kashin da mafi akasarin shugabannin da suka rike madafun iko na kasar, suka yi watsi da kyawawan shiriye-shirye da tsare-tsaren da tsaffin ministocin su ma suka samar a lokacin da suka shugabanci ma’aikatar, inda suke kawo nasu tsare-tsaren da kuma shiye-shiyen da suke bukata.
Misali, shirin inganta noman Rogo; wanda Adamu Bello ya kirkiro a lokacin da ya shugabanci ma’aiktar, wanda kuma bayan nada Dakta Adesina a matsayin ministan ma’aikatar, ya kara karfafa shirin.
Sai dai abin takaic, shirin bai kai labari ba; wanda kuma Naira biliyan 10 da aka zuba domin renon gonakin noman na Rogon, ba a iya warware takaddamar kudin da aka ware wa aikin ba.
Haka zalika, Adesina ya kirkiro da wani tsari na tura wa manoma kudin tallafin aikin noma kai tsaye zuwa asusun ajiyarsu na bankuna, musamman domin kawar da ayyukan ‘yan-na-kama.
Sai dai abin takaici, a lokacin da Cif Audu Ogbeh ya karbi ragamar ma’aikatar, ya yi watsi da wannan tsari na Adesina, musamman saboda dimbin bashin kimanin Naira biliyan 76 da aka gada daga wurin tsohuwar gwamnatin tsohon shugaban kasa, Gooluck Jonathan.
Kwararru da dama a fannin aikin noma na kasar nan, sun yi amanna da cewa, daukacin wadannan tsoffin ministoci 54, babu wani kokari da suka yi na kara ciyar da fannin gaba; duba da yadda kasashe kamar Indiya, Pakistan da Brazil suka yi wa Nijeriya fintinkau a fannin farfado da aikin noma.
Wasu daga cikin kwararru kamar Dakta Aliyu Sumaila, ya bayyana dalilan da suka sanya aka gaza samar da sauyi a wannan fanni na noma, wadanda suka hada da yin noma da kayan aiki na gargajiya; wanda hakan yasa ba a samun girbin amfani mai yawa da rashin yin amfani da kayan noma na zamani, wanda hakan ke jawo wa manoma yin asara a girbin farko na amfanin gonakinsu.
Shi kuwa, Farfesa Banji Oyelaran-Oyeyinka, mai bai wa Shugaban Bankin Raya Nahiyar Afirka (AfDB) shawara ya bayyana cewa, kasar ta gaza samar da sauyi a fannin aikin noman ne sakamakon yadda ‘yan siyasa suka yi watsi da shiye-shiyen da aka kirkiro na habaka fannin, saboda son zuciyarsu.
A cewar tasa, kasashe kamar Indiya Fakistan, Birazil da kuma Bietnam; wadanda suka kasance cikin sahu na gaba a kan Nijeriya a fannin noma, sun samu ci gaba wajen samar da sauyi a fannin nasu.
Banji ya ci gaba da cewa, akwai babbar tazara tsakanin Nijeriya da Kasar Birazil wajen girbe amfanin gona, inda ya bayyana cewa; idan har Nijeriya na son cike wannan gibi, ya zama wajbi ta rungumi noma da kayan aiki na zamani tare kuma da samar da ingantaccen Irin noma da kuma kara bunkasa noman rani.