Gabatarwa:
Ana sarrafa Citta zuwa wasu nau’ikan kayan lemon kwalba ko ganyen shayi da sauran makamantansu.
Kazalika, a daukacin fadin duniya; ana sarrafa Citta zuwa nau’ikan magungunan gargajiya, ana kuma sarrafa ta zuwa nau’ikan wasu magunguna na Bature, wanda mutane ke amfani da su don neman lafiya.
Har ila yau, ana sarrafa Citta zuwa nau’ikan magungunan da ake bai wa dabbobi kamar Dokuna, Shanu, Rakuma da sauransu.
Tarihi ya nuna cewa, an fara yin noman Citta a Nijeriya tun a shekarar 1927, bayan gudanar da wani bincike; domin gano amfanin gonar da zai bai wa mazauna Kudauncin Kaduna damar yin kasuwancin cikin gida, musamman yankin na da albarkatun Citta.
Daga 1967 zuwa 1998 harkar noman Citta, ya ragu kwarai da gaske sakamakon wasu tsare-tsare da kuma yin watsi da fannin da gwamnati ta yi da kuma rashin samun kudaden shiga daga fannin, musamman biyo bayan samun danyen mai a kasar nan.
Bisa nazarin da wani masani mai suna Hokiet ya yi a 1992 da kuma nazarin da wani masanin Yohanna ya yi a 2007, sun nuna cewa; za a iya samun cin nasara a fannin aikin noma ta hanyar amfani da fasahar zamani na yin noman wannan Citta, wanda hakan zai taimaka wajen kara bunkasa fannin da kuma habaka tattalin arzikin kasa.
Matsayin Noman Citta A Nijeriya:
Nijeriya na da wadatacciyar kasar noman Citta, musamman kamar yadda hukumar abinci ta duniya (FAO) ta sanar.
Hukumar ta ce a 2009, kimanin kasahi 45.4 a cikin dari; kadada daya tak ta Cittar aka noma.
Kazalika, hukumar ta bayyana cewa, Cittar da aka girbe a Nijeriya a 2009 ta kai kimanin tan 3.4, wanda hakan ya nuna cewa, an samu raguwar a girbinta kwarai da gaske, idan aka kwatanta da yadda wasu sassan duniya suke a halin yanzu.
A kimiyyance, ana iya noman Cittat a kowane sashe na kasar nan, amma akasari an fi nomanta a Jihohin Kaduna, Nasarawa, Benuwe, Neja da kuma Gombe.
A halin yanzu, yankin Kudancin Kaduna ne ke samar da Citta sama da kashi 95 cikin dari.
Noman Citta A Zamanance:
Kayan aikin noma da suka hada da ingantacciyar kasar noma, gudanar da bincike, ilimin zamani, sadarwa, samar da bayanai, fasahar zamani da kuma taraktocin noma, na matukar bayar da gudunmawa wajen habaka noman Citta.
Rashin samar da wadannan kayan aiki kuwa, na karya wa manoma kwarin guiwa tare da gaza samar da wadataccen amfanin gona; kari a kan hakan kuma shi ne, zai iya haifar da talauci, musamman a tsakanin kananan manoma.
Sai dai, fannin noman Citta a Nijeriya, bai samu kulawar da ta dace ba, wanda hakan ya sanya akasari ana yin nomanta ba tare da yin amfani da kayan noma na zamani ba.
Har ila yau, manyan manoman Cittar su ne ke yin amfani da taraktar noma wajen gyaran gona da yin haro da sauran makamantansu.
Hatta kananan manoman da ke noma ta, wadanda su ne suka fi yawa, har yanzu suna yin nomanta ne a gargajiyance.
Kalubalen Da Ke Tattare Da Noman Citta:
Abubuwa da dama ne suka taru suka haifar wa da noman Citta kalubale, wadanda suka hada da rashin samar da kyakkyawan tsari daga wurin gwamnati, rashin kwarewa, nuna halin ko in kula; wanda hakan ke durkusar da masu son zuba jari wajen nomanta a zamanance.
Haka zalika, tsare-tsare da dama a gwamnati, sun janyo kalulabe a fannin wannan noma, wadanda suka hada da Rogo, Kwakwar Manja, Auduga da sauransu.
Sai dai, domin a kara habaka noman a zamanance, gwamnatin tarayya ta kirkiro da cibiya ta kasa mai kula da harkar noman nata a zamanance da ke a garin Ilorin, wato (NCAM) a 1975 zuwa 1980.
Duk da cewa, wannan cibiyar ta yi iya kokarinta, amma kananan manoman Citta ba sa iya samun kayan aiki na zamani.
Alfanun Da Ke Tattare Da Noman Citta:
Allah ya albarkaci Nijeriya da wadatacciyar kasar noma, wadda kuma za a iya yin noman Citta mai tarin yawa.
Kazalika, ta na da wadatattun albarkatu; wadanda da an yi amfani da su, za su samar da damar yin fasahar yin kasuwanci wajen yin noman wannan Citta.
Manoman Citta a Nijeriya, kansu a hade yake; sannan kuma suna kara samun fadakarwa, wanda idan aka ci gaba da fadakar da su tare da samar musu da tallafi da kudade, musamman wajen rungumar yin nomanta a kamiyyance, ko shakka babu za su samu dimbin alfanu daga wannan fanni.
Sai dai, ta hanyar kirkiro da tsare-tsare masu kyau wanda gwamnati ta yi, hakan ya sa manomanta samun dauki na kudade ta hanyar bankin CBN.
Bugu da kari, a kwanakin baya; an sanya Citta a jerin amfanin gonar da za ta samu kulawa ta musamman daga shirin habaka fannin aikin noma na (ATA), wanda gwamnati mai ci ta kirkiro da shi.
Maiyiwuwa wannan yunkuri na gwamnati, ya taimaka wajen kara noman wannan Citta a kimiyance tare da nomanta, domin samun riba a wannan kasa.