• English
  • Business News
Saturday, September 13, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Nazari Kan Taraktoci 2,000 Da Tinubu Ya Kaddamar Don Bunkasa Noma

by Abubakar Abba
2 months ago
in Noma Da Kiwo
0
Nazari Kan Taraktoci 2,000 Da Tinubu Ya Kaddamar Don Bunkasa Noma
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsAppTelegram

A kokarin Nijeriya na samar da sauyi, domin inganta fannin aikin noma, a ranar 23 ga watan Yunin 2025 ne, gwamnatin shugaba Bola Tinubu, ta kaddamar da Taraktocin noma 2,000.

Ta kaddamar da Taraktocin ne, karkashin shirin nan na gwamnatinsa ‘Renewed Hope’, don aiwatar da noma zamani.

  • Rashin Ganin Shugabannin APC Yayin Ziyarar Shettima A Kano Ya Haifar Da Zazzafar Muhawara
  • 2027: Takarar Shugaban Kasa Zan Yi Ba Mataimaki Ba – Peter Obi

Gwamatin ta yi hakan ne, domin kara bunkasa aikin noma da samar da wadataccen abinci a fannin aikin noma, domin samun riba.

Kaddamar da Taraktocin, ya nuna irin kudurin gwamnatin; na komawa aikin noma tare kuma da amfani da kayan noman na zamani.

A cewar fadar shugaban kasa, gwamnatin ta samar da wannan dauki ne, domin cike gibin da kasar ke da shi na karancin kayan aikin noma na zamani tare kuma da kara habaka fannin aikin noma.

Labarai Masu Nasaba

Nazari Kan Bukatar Manoma Su Rika Yi Wa Mangwaro Ban-ruwa

Muna Bukatar Karin Hekta 500,000 Domin Noman Kwakwar Manja – POFON

Har ila yau, manufar ita ce; don rage yawan asarar da manoma ke tabkawa, bayan sun yi girbin farko da kuma jawo hankalin matasan kasar, domin su rungumi aikin na noma; musamman wanda za su yi, su samu riba.

Kaddamar da Taraktocin na zuwa ne, daidai da lokacin da kasar ke ci gaba da fuskantar hauhawar farashin kayan abinci, wanda ya kai sama da kashi 30 cikin 100, duba da cewa; noman da ake yi a karkara na ci gaba yin karanci.

Idan har an rabar da wadannan Taraktoci yadda ya dace tare da horar da manoman da za su amfana, an kuma tabbatar da ana bai wa Taraktocin kulawar da ta kamata da sayar da su cikin rahusa, hakan zai taimaka wajen samun kyakkyawan sauyi a fannin noman kasar, musamman a bangaren samun riba.

Sai dai, har yanzu; tambayar da ake ci gaba da yi ita ce, shin ko wannan shiri zai samar da kyakkyawan sauyi a fannin na aikin noman kasar?

Hakikanin Fannin Aikin Noma Don Samun Riba A Nijeriya:

Fannin aikin noman kasar, na samar da ayyukan yi sama da kashi 70 cikin 100, inda kuma fannin ya kasance kimanin kashi 34 cikin 100 na aikin da ake yi a kasar.

Amma duk da haka, har yanzu fannin kashi 26 kacal yake bayarwa a matsayin gudunmawa, don bunkasa tattalin arzikin kasar, wanda akasari hakan na faruwa ne, sakamakon yadda ake yin noma da kayan aiki na gargajiya.

Nijeriya da ke Afirka ta Kudu da Hamada, aikin nomanta ya yi kasa sakamakon rashin yin aiki da kayan noma na zamani. Ta kuma kasance, tana da kasa da karamin ma’auni na hekta da ya kimanin 0.3, wanda hakan ya saba da shawarar da Hukumar Kula da Abinci da Ayyukan Noma ta Majalisar Dinkin Duniya (FAO) ta bayar na bukatar samar da hekta 1.5 na yin noma.

Bugu da kari, an rawaito Mataimakin Shugaban Kasa, Sanata Kashim Shettima ya bayyana cewa; Nijeriya mai yawan al’umma sama da miliyan 210, amma abin takaici, kasar na da Taraktocin noma masu aiki daga tsakanin 7,000 zuwa 12,000 ne kacal.

A cewarsa, hakan ya sanya a shekaru da dama da suka gabata, aka gaza samun bukatar da ake da ita ta samar da yawan abincin da ya kai mililiyan 2.4, domin bukatar ‘yan kasar.

Sai dai, ana ganin bisa wannan sabon yunkuri na gwamnatin ta hanyar hadaka da kamfanin kera kayan aikin noma da ke Belarus, wanda aka kaddamar da aikin tare da AfTrade DMCC, hakan ya sa an samar da ingantattun Taraktocin noma 2,000 tare da samar da kayan haro 190 da sauran makamantansu.

A karkashin aikin, ana sa ran za a noma hektar noma sama da 550,000, wadanda za su samar da tan miliyan 2 na hatsi tare da samar da ayyukan yi, wadanda ba na kai tsaye ba kimanin 16,000 da kuma na kai tsaye kimanin sama da 550,000.

Kaddamar da Taraktocin da sauran kayan aiki, hakan zai taimaka wajen habaka aikin noma don samun riba da kara bunkasa samar da wadataccen abinci da rage shigo da kayan abinci cikin Nijeriya, wanda yanzu haka, wadanda ake shigo da su a duk shekara, kudinsu ya kai sama da dala biliyan 2.5

Samar Da Wadataccen Abinci Da Matsalar Samun Hauhawar Farashin Kayan Abinci A Nijeriya:

Duk da samar da albarkar hektocin noma da Nijeriya ke da su, wadanda suka kai miliyan 70.8 kuma ake noma amfanin gona kamar irin su; Masara, Rogo, Shinkafa da saurasu, amma kasar na ci gaba da fuskantar hauhawar farashin kayan abinci.

Fannin shi ne kusan kashin bayan bunkasa tattalin arzikin kasar, amma sama da ‘yan kasar miliyan 100 ne a yanzu ke fuskantar karancin abinci, kuma suna ci gaba da fuskantar hauhawar farashin kayan na abinci da kuma rashin wadatattun kudaden sayen kayan abincin.

Wannan adadin, ya nuna yadda yanayin hauhawar farashin ya yi kamari, musamman a Arewa ta Tsakiyar kasar, wanda ya kai kashi 29.43 a Arewa ta Gabas, ya kai kashi 29.72.

Bugu da kari, kididdiga ta nuna cewa; ‘yan Nijeriya miliyan 18.6 ke ci gaba da jure wa yunwa, inda kuma mutane miliyan 43.7, suka dauki matakin rage cin abincin da suke ciyar da iyalansu.

‘Yan Nijeriya miliyan 133 ke ci gaba da fuskantar karancin ababen more rayuwa tare da ci gaba da fuskantar hauhawar farashin kayan abinci, wanda a watan Mayun 2025 ya kai kashi 21.14 tare da kuma fuskantar matsananciyar yunwa.


Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

Tags: Noma
ShareTweetSendShare
Previous Post

Rashin Ganin Shugabannin APC Yayin Ziyarar Shettima A Kano Ya Haifar Da Zazzafar Muhawara

Next Post

Dalilin Ware Naira Biliyan 19.5 Da Asusun Bunkasa Aikin Noma Ya Yi

Related

Nazari Kan Bukatar Manoma Su Rika Yi Wa Mangwaro Ban-ruwa
Noma Da Kiwo

Nazari Kan Bukatar Manoma Su Rika Yi Wa Mangwaro Ban-ruwa

7 days ago
Muna Bukatar Karin Hekta 500,000 Domin Noman Kwakwar Manja – POFON
Noma Da Kiwo

Muna Bukatar Karin Hekta 500,000 Domin Noman Kwakwar Manja – POFON

7 days ago
Gwamnatin Tarayya Na Hasashen Samun Naira Biliyan 300 Kan Noman Dabino A Yobe
Noma Da Kiwo

Gwamnatin Tarayya Na Hasashen Samun Naira Biliyan 300 Kan Noman Dabino A Yobe

3 weeks ago
Ya Zama Wajibi Nijeriya Ta Cimma Wa’adin Tura Cocoa Tarayyar Turai A Disambar 2025
Noma Da Kiwo

Ya Zama Wajibi Nijeriya Ta Cimma Wa’adin Tura Cocoa Tarayyar Turai A Disambar 2025

3 weeks ago
Kwararre Ya Ja Hankali Kan Sayar Da Takin Zamani Da Ba A Tantace Shi Ba
Noma Da Kiwo

Kwararre Ya Ja Hankali Kan Sayar Da Takin Zamani Da Ba A Tantace Shi Ba

4 weeks ago
Manoman Doya 100 A Jihar Nasarawa Suka Amfana Da Horon Cibiyar NEPC
Noma Da Kiwo

Hukumar NABDA Ta Bukaci Musulmi Su Cire Fargabar Amfani Da Fasahar Alkinta Halittu

4 weeks ago
Next Post
Wa’adin Da Tinubu Ya Bai Wa Manoman Da Suka Ci Bashin ‘Anchor Borrowers’ Ya Cika

Dalilin Ware Naira Biliyan 19.5 Da Asusun Bunkasa Aikin Noma Ya Yi

LABARAI MASU NASABA

Tsawon Hanyoyin Jiragen Kasa A Biranen Sin Ya Zama Na Farko A Duniya

Tsawon Hanyoyin Jiragen Kasa A Biranen Sin Ya Zama Na Farko A Duniya

September 12, 2025
Tawagogin Sin Da Amurka Za Su Tattauna A Spaniya

Tawagogin Sin Da Amurka Za Su Tattauna A Spaniya

September 12, 2025
Kamfanonin Kasashen Waje Za Su Ci Gaba Da Habaka Harkokinsu A Sin

Kamfanonin Kasashen Waje Za Su Ci Gaba Da Habaka Harkokinsu A Sin

September 12, 2025
Kamfanonin Kasashen Waje Za Su Ci Gaba Da Habaka Harkokinsu A Sin

Kamfanonin Kasashen Waje Za Su Ci Gaba Da Habaka Harkokinsu A Sin

September 12, 2025
Shugaban Ghana: Manufar Soke Biyan Harajin Kwastam Ta Kasar Sin Ta Ba Da Damammaki Ga Afirka

Shugaban Ghana: Manufar Soke Biyan Harajin Kwastam Ta Kasar Sin Ta Ba Da Damammaki Ga Afirka

September 12, 2025
Gwamna Lawal Ya Tallafa Wa Ƙananan ’Yan Kasuwa Da Sama Da Naira Biliyan Ɗaya

Gwamna Lawal Ya Tallafa Wa Ƙananan ’Yan Kasuwa Da Sama Da Naira Biliyan Ɗaya

September 12, 2025
Akpabio Da Abbas Sun Yi GargaÉ—i Kan Ciwo Bashi Ba Tare Da Sa Ido

Akpabio Da Abbas Sun Yi GargaÉ—i Kan Ciwo Bashi Ba Tare Da Sa Ido

September 12, 2025
Yawan Yarjejeniyar Zuba Jari Da Aka Kulla a CIFIT Ya Kai 1154

Yawan Yarjejeniyar Zuba Jari Da Aka Kulla a CIFIT Ya Kai 1154

September 12, 2025
Korafin Philippines Ya Tabbatar Da Halascin Matakan Da Sin Ke Dauka Na Kare Muhalli a Tsibirin Huangyan

Korafin Philippines Ya Tabbatar Da Halascin Matakan Da Sin Ke Dauka Na Kare Muhalli a Tsibirin Huangyan

September 12, 2025
‘Yan Bindiga Sun Sace Mutum 7 A Jihar Neja

‘Yan Bindiga Sun Harbi Fasinjoji 2 A Jihar Neja

September 12, 2025
Talla

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In

Add New Playlist

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.