Daga Idris Umar,
Har yanzu ana cigaba da jajenta rasuwar shugaban kamfanin LEADERSHIP, Marigayi Sam Nda-Isaiah, Kakakin Nupe, inda Magajin Garin Nupe, Farfesa Ahmad Abdallah Dangi, tsohon Ministan Aikin Gona a Tarayyar Nijeriya, ya siffanta maraigayin a matsayin mutumin kirki a lokacin rayuwarsa.
Magajin Garin Nupen ya bayyana hakan ne a tattaunawarsa da Wakilin LEADERSHIP A YAU yana mai cewa, “a gaskiya duk wanda ya san Sam ya san shi ne a matsayin mutum mai mutunci da sanin ya kamata.
“Bayan haka na yi tarayya da shi a bangarori da dama. Daga ciki akwai harkar sarauta, domin shine Kakakin Nupe. Bayan haka mun yi gwagwarmayar neman ‘yancin samun cigaba a jiharmu. Kuma yana cikin gwagwarmayar nemawa Nufawa jiha mai suna Nda Duma, wanda lokuta da dama, saboda himma irin tashi ne ma kwamiti ya ba shi matsayin mai masaukin baki. Saboda a muhallinsa na Abuja muke gudanar da meeting duk lokacin da lamarin ya taso.
“Sam mutum ne mai biyayya, duk da yake a harkar duniya shi dan APC ne, ni kuma dan PDP ne, amma hakan bai sa ya zubar da zumuncin da ya ke yi da jama’arsa, wanda ya kai shi ga har ya yi takarar shugabancin wannan kasa tamu.
“Kuma shi kansa mahaifinsa mun yi zaman mutunci da shi a matsayin ‘yan uwa. Wannan kyawun dabi’a ta Sam ya sa ake girmama shi ko a kwamitinmu na neman jiharmu mai suna Nda Duma. Don haka babu wani abu da na sani game da wannan yaro, illa abin alkairinsa a gida da waje.”
Daga nan ne kuma sai Magajin Garin Nupen ya mika sakon ta’aziyyarsa ga iyalin marigayin da ma’aikatan LEADERSHIP bakidaya.