Daga Khalid Idris Doya,
Hukumar hana sha da fataucin miyagun kwayoyi wato (NDLEA) reshen hukumar da ke Edo, a jiya ne ta shaida cewar ta samu nasarar kame mutum dari biyu da sittin da biyu (262) bisa zarginsu da kasance dillalan miyagun kwayoyi wadanda ta kamasu tare da kilogram din miyagun kwayoyi masu sanya maye 15,253.82kg wadanda suka kunshi wiwi, hodar iblis, da kuma Tiramadol a shekarar da ta gabata.
Hukumar ta ce, daga cikin wadanda ta kaman, 180 maza ne, yayin da kuma 82 suka kasance mata, inda aka kama kayan cikin motoci guda 10 da suka yi amfani da su wiring fasa kwabrin miyagun kwayoyi gami da jigilarsu, har-ila-yau, ta kuma lalata da tarwatsa gonar Wiwi 15 mai girman hekta 11.82 dukka a cikin shekarar da ta shude.
Hukumar ta lura kan cewa, mutum 86 daga cikinsu an gargadesu da ja musu kunne bayan lura da batutuwansu tare da sallamarsu don su koma ga iyalansu, a yayin da kuma aka yanke wa dillalan miyagun kwayoyi 8 hukunci, sauran kesa-kesai 220 kuma suna gaban babban kotun tarayya har zuwa ranar 31 ga watan Disamban 2020.
Ya ce, dukkanin dabarun da dillalan miyagun kwayoyi suke bi wajen safaran kayansu, hukumar ba za ta zura ido ba, za ta ci gaba da kokarinta na tabbatar da dakile aniyarsu.
Buba ya jinjina wa Gwamnan jihar Godwin Obaseki, bisa hanzarin samar da muhallin wucin gadi wa hukumar bayan da masu zanga-zangar #EndSARS din suka tarwatsa musu shalkwata a watan Oktoban shekarar da ta shude.