Hukumar yaki da sha da fataucin miyagun kwayoyi ta kasa NDLEA, ta cafke wani dan kasuwa, Molokwu Nwachukwu, wanda ke yawan zuwa kasashen China, Dubai, Pakistan, da Vietnam a wani yunkurin fitar da hodar iblis a filin jirgin sama na Murtala Muhammed (MMIA) da ke Ikeja, Legas.
An kama wanda ake zargin ne da boye kullin hodar ibilis guda 36 a sassa daban-daban na jakunkunansa da jakar hannu da silifas wari biyu a lokacin da ya nufi kudu maso gabashin Asiya.
Kakakin hukumar ta NDLEA, Femi Babafemi, ya ce an kama Molokwu a wurin tantance kaya bangare na biyu a tashar a yayin da yake yunkurin hawa jirginsa zuwa Vietnam a ranar Laraba, 22 ga Maris, 2023.