Hukumar NDLEA a Kano ta kama kwalabe 8,000 na Akuskura da ake zargin na ɗauke da ƙwayoyi, tare da tabar wiwi guda 48.
An cafke wani mutum mai shekara 37, Ali Muhammad, bayan an gano kayan a cikin tirela É—auke da kekuna a kan hanyar Zariya zuwa Kano a Gadar Tamburawa.
- ’Yansanda Sun Kama Masu Safarar Makamai A Katsina, Sun Ƙwato Makamai
- ’Yansanda Sun Kama ‘Yan Daba 107 A Kano, Sun Ƙwato Makamai Da Ƙwayoyi
NDLEA ta ce tana tsare da wanda ake zargin da kuma kayayyakin, yayin da ake ci gaba da bincike.
Hukumar ta buƙaci jama’a su riƙa sanar da ita duk wani abin da suka zarga na da alaƙa da miyagun ƙwayoyi.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp