Hukumar yaƙi a sha da fataucin miyagun ƙwayoyi (NDLEA) reshen Jihar Kano ta kama wani tsoho mai shekaru 75, Nuhu Baba, bisa zargin sayar da miyagun ƙwayoyi ga matasa.
Jami’in hulɗa da jama’a na hukumar, Sadiq Muhammad-Maigatari, ne ya bayyana hakan cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Talata a Kano, inda ya ce wanda ake zargi ya amsa laifinsa, yana mai cewa ya rungumi sana’ar ne domin rayuwa a unguwarsu da ke ƙaramar hukumar Gezawa.
- NDLEA Ta Cafke Masu Ta’ammali Da Ƙwayoyi 18,500 A 1 – Marwa
- NDLEA Ta Gargadi Iyaye Kan Bayyanar Alawar Ƙwaya A Kano
Hukumar ta kwato nau’ikan kwayoyi daban-daban, ciki har da Tramadol, wiwi, Diazepam, Exol-5 da man shafawa mai sa maye. Kakakin hukumar ya ce Kwamandan NDLEA na Kano, Abubakar Idris-Ahmad, ya jaddada ƙudurin hukumar na yaƙi da sha da fataucin ƙwayoyi tare da buƙatar hadin gwuiwar al’umma domin daƙile wannan matsala.