Hukumar hana sha da safarar miyagun kwayoyi (NDLEA) ta kwace miyagun kwayoyi da kudinsu ya kai kimanin naira biliyan 450 tare da damke masu safarar kwayoyi guda 23,907 a tsakanin watan Janairun 2021 zuwa watan Oktobar 2022.
Shugaban hukumar NDLEA, Buba Marwa shi ya bayyana hakan a warin bikin karramawa na karshen shekara da bayar da lambar yabo da kara wa jami’ai girma, wanda ya gudana a harabar shalkwatar hukumar NDLEA da ke Abuja.
- INEC Za Ta Dauki Hayar Motocin Sufuri 100,000 Da Jiragen Ruwa 4,200 Don Raba Kayan Zabe – Yakubu
- Da Dumi-Dumi: Saudiyya Ta Bai Wa Nijeriya Gurbin Mahajjata 95,000 A Hajji Mai Zuwa
Ya kara da cewa a lokacin gudanar da wannan bincike, hukumarsa ta samu nasarar cafke masu safarar miyagun kwayoyi guda 23,907 ciki har da hodar Iblis 29.
“Mun kwace sama da tan miliyan 5,500 ko kilogiram miliyan 5.5 na miyagun kwayoyi wanda tsabar kudinsu ya sama da biliyan 450.
“A wannan lokacin dai, mun lalata konar wiwi da ta kai eka 772.5.
“A cikin watanni 22, mun samu nasarar gurfanar da masu laifi har guda 3,434 a gaban kuliya.
“A konarinmu na yakin da miyagun kwayoyi, mun samu nasarar gyara tunanin mutum 16,114 wadanda suka kasance suna ta’ammuli da miyagun kwayoyi,” in ji shi.
Ya kara da cewa ayyukan da hukumarsa ta yi a tsawan watanni 22 ya dace ta gudanar da irin wannan biki.
Marwa ya ce wannan alkaluma da aka bayyan kididdiga ne kwai sai mutum ya yi nazari zai iya ganin irin cutarwar da suke yi wa al’umma. Ya ce za su yi matukar illa ga lafiya da kuma tsaro idan har aka bari wadannan miyagun kwayoyi suka shiga kan hanya.
A cewarsa, hukumar NDLEA ta kwace kwayar tiramado miliyan 100, ya ce idan har da wadannan kwayoyi sun kai ga kan hanyoyi, za su isa hannun masu sayarwa wanda babban illa ce ga al’umma.
“Wannan lamari yana da matukar matsala ga rayuwa, iyali da harkokin samarwa, saboda suna matukar illa ga matasa wanda su ne kashin bayan samar da kowani abu a kasar nan.
“Mun yi wannan nazari ne domin mu bayar da lambar yabo da karrama da karin matsayi bisa irin namijin kokarin da jami’anmu suka gudanar,” in ji shi.
Da yake mika lambar yabo da takardun karin girma ga jami’an NDLEA, Marwa ya bukaci su rike wannan lambar yabo a matsayin wasiyyar kwarewa na samun nasara.
Ya ce, “NDLEA za ta ci gaba da karrama wadanda suka bayar da gagarumar gudummuwa ga hukumar. Mun karrama jami’ai guda 3,506 a shekarar da ta gabata kuma ba nan za mu tsaya ba.
Marwa ya ce karin girma ya kasance lada ne na hukuma wanda take bayarwa ga gwarazan da suka nuna bajinta lokacin gudanar da ayyukansu. Ya ce ana bayar da shi ne ga wadanda suka cancanta kadai saboda su kara jajircewa wajen gudanar da ayyukan da aka dora musu.
Haka kuma ya ci gaba da cewa ba kowani jami’i ba ne ya cancanci a kara masa girma daga mukamin da ya kasance zuwa wani mukami na sama, sai dai wadanda suka cancanta ne kadai suke samun wannan dama.
Hukumar NDLEA ta kara wa jami’anta girma har guda 1,018, wadanda suka hada da manyan mataimakan kwamandoji guda da biyu. Haka kuma an kara wa jami’ai 17 da aka ba su sabon mukami na manyan mataimakan kwamandoji masu yaki da miyagun kwayoyi da kwamandoji 29 da matsakaitan mataimakan kwamandoji 78 da kuma sauran kananan mataimakan kwamandoji 111.
Sauran sun hada da babban sufuritanda 63 da sufuritanda 106 da kuma mataimakan sufuritanda 129. Akwai kuma wasu jami’ai guda 25 da aka ba su mukaman mataimakan sufuritanda na daya da kuma mataimakan sufuritanda na biyu guda 400.