A Sanatan da ke wakiltar Borno ta Kudu, Sanata Muhammad Ali Ndume, ya kaddamar da fara bada tallafi wa mata 1,200 wadanda daga cikinsu akwai Zawarawan da ‘yan Boko Haram suka kashe mazajensu.
Matan sun samu tallafin Kekunan Dinki, Injunan Nika da kuma kudade a hannu da aka ba su domin tsayuwa da kafafunsu.
A cewar sanarwar ofishin yada labarai ta Ndume wanda ya rabar a Abuja, ta yi bayanin cewa mataimakin gwamnan jihar Borno, Umar Usman Kadafur shi ne ya mika kyautukan kayan ga matan da suka samu cin gajiyar da suka kunshi Zawarawa sama da 100, wanda suke daga shiyyar Borno da kudu a farkon rabon kayan tallafin.
Shirin baiwa mata tallafin ya gudana ne a dakin taro na Ambassador Lodge da ke karamar hukumar Biu, sannan matan sun kuma amfana da tallafin kudi da ya kai naira miliyan uku wanda aka raba musu kyauta.
Maitaimakin gwamnan Alhaji Kadafur ya bukaci matan da su ka amfana da tallafin da kada su saida su yi kokarin tsayuwa da kafafunsu ta hanyar yin sana’o’in hannu.
Matan da suka amfana sun fito ne daga kananan hukumomin Biu, Hawul, Kwaya, Bayo da karamar hukumar Shani.
Sanarwar ta ce aikin rabon kashi na biyu zai shafi mata 600 da zai gudana a Askira/Uba domin raba wa matan da za su fito daga Chibok, Damboa da karamar hukumar Gwoza.