Babban daraktan gudanarwa na hukumar bunkasa shiyyar Arewa Maso Gabas (NEDC), Mohammed G. Alkali, ya nuna aniyar hukumar na yin hadin guiwar Gwamnatin jihar Bauchi domin labibo hanyoyin magance ambaliyar ruwa domin kiyaye barnar da hakan ka iya yi a nan gaba a fadin jihar.
Alhaji Mohammed G. Alkali ya yi bayanin cewa sun zo jihar Bauchi a ranar Laraba ne domin mika kyautar kayan abinci da wasu kayan bukatun yau da gobe ga wadanda ambaliyar ruwa ta shafa domin rage musu radadin halin da suke ciki a jihar ta Bauchi.
Goni, ya kuma kara da jajanta wa gwamnati da al’ummar jihar bisa wannan ambaliyar ruwa da ta shafi jihar a bana da ya shafi wasu sassan jihar.
Ya yi bayanin kayan abinci da na sanyawa da suka bai wa jihar da cewa sun hada da buhunan shinkafa dubu 10 (10,000), bargunan rufuwa guda 5,000, atamfa na mata guda 5,000, shadda na maza guda 3,000, tabarma guda dubu biyar (5,000), galan din Mangeda guda 3,000, rigunan yara guda 3,000 da kuma dukka an mika su ga Gwamnatin jihar Bauchi da nufin rabawa ga wadanda lamarin ya shafa.
MD, ya jinjina wa gwamnan Jihar Bauchi bisa kokarinsa na taimakawa ga wadanda ambaliyar ta shafa, ya yi fatan kayan abinci da wadanda ba na abincin da suka kawo jihar za su rage radadin tare da tallafawa ga wadanda ambaliyar ta shafa a jihar.
Alhaji Goni daga bisani ya yi magana kan ayyukan da hukumar ke gudanarwa a jihar Bauchi da suka hada da aikin hanyar Kirfi zuwa Gombe Abba, da ayyuka a sashin Ilimi, lafiya da sauran fannoni gami da saura da dama.
“Sannan, muna da aikin gina gidaje da ake ciki gaba da yi, sannan da aiki a daya daga cikin manyan cibiyoyin ilimi da na lafiya na jiha ko na tarayya, da kuma ayyukan su na cigaba da gudana.”
A nasa fannin, gwamna Bala Muhammad na Jihar, ya nuna matukar farin cikinsa bisa wannan tallafin da hukumar ta bai wa jihar, yana mai cewa samar da hukumar NEDC na daga cikin muhimman tarihi da nasarorin da shugaban kasa Muhammadu Buhari ya kafa a zamansa Shugaban kasa.
Ya ce, hukumar na daga cikin rassan da ke gudanar da ayyukansu da ke zuwa ga talakawa da al’umma kai tsaye, kuma sa a jima ana amfanuwa da ayyukan da suke gudanarwa.
Ya kuma jinjina kan yadda hukumar ke gudanar da ayyukanta na farfado da shiyyar Arewa Maso Gabas da hare-haren Boko Haram ya daidaiya a shekarun baya.
Gwamna Bala ya sanar da bakin nasa cewa tabbas ambaliyar ruwa ta yi barna sosai a jihar, ya nuna cewa hatta shi kansa da Gwamnatinsa sun yi kokarin samar da tallafin gaggawa ga wadanda lamarin ya shafa, ya nuna cewa lamarin ne ya yi yawa sosai amma sun yi kokari sosai wajen samar da nasu tallafin a matakin jihar.
Kan hakan ne ya nuna cewa kayan tallafin abinci da na wadanda ba abinci ba da suka samu daga hukumar za su taimaka sosai ga wadanda ambaliyar ta shafa.
Kana, ya jinjina da ayyukan da hukumar ke gudanarwa a jihar da cewa tabbas hakan na taimaka wa rayuwar al’ummar jihar.
Daga bisani ne kuma MD, Alkali ya mika kayan tallafin da suka kawo jihar ta hannun mataimakin gwamnan Jihar Bauchi Sanata Baba Tela da nufin rabawa ga wadanda lamarin ya shafa.