Gwamnatin tarayya ta ceto wasu mutane bakwai da suka makale a wani wajen hakar ma’adanai a yankin Galadima Kogo da ke karamar hukumar Shiroro ta Jihar Neja.
Ministan ma’adanai, Dele Alake ne, ya bayyana hakan a wata sanarwa da mai taimaka masa na musamman kan harkokin yada labarai, Segun Tomori ya fitar ranar Talata a Abuja.
- ‘Yan ta’adda 176 Sun Mika Wuya, An Cafke 57 A Tafkin Chadi – MNJTF
- Hajj 2024: Jihar Kaduna Ta Kammala Jigilar Maniyyata Fiye Da 4,000 Zuwa Saudiyya
Ya ce tuni aka tura masu bayar da agaji zuwa wajen da lamarin ya faru, inda ya kara da cewa ana aikin ceton tare da hadin gwiwar kamfanin hakar ma’adanai.
Kamfanin dillancin labaran Nijeriya (NAN), ya ruwaito cewa mutane 30 ne, suka makale cikin ramin da ake hakar ma’adanai da kamfanin African Minerals and Logistics Ltd ke aiki.
NAN ya kara da cewa, Alhaji Abdullahi Arah, Darakta-Janar na Hukumar Bayar da Agajin Gaggawa na Jihar Neja (NSEMA), ya ce lamarin ya faru ne sakamakon mamakon ruwan sama.
Ministan ya ce kokarin da gwamnatin tarayya ke yi ya nuna yadda ta himmatu wajen ganin an dakile asarar rayuka, da kuma ceto wadanda suka makale.
“Da samun labarin faruwar lamarin, sai muka tura jami’an kula da ma’adanai na tarayya (FMO) da jami’an hukumar binciken ma’adanai wajen.
“Tare da hadin gwiwar kamfanin hakar ma’adanai, mun ceto mutane bakwai da suka makale. Ana ci gaba da gudanar da aikin ceto a wajen,” in ji shi.
Ya kuma bai wa ‘yan Nijeriya tabbacin gwamnatin tarayya ta kuduri aniyar yin bincike kan musabbabin afkuwar lamarin.