Hukumar ba dalibai bashin kudin karatu ta ce dalibai miliyan daya ne suka nemi a basu bashin kudin karatu daga kafar sadarwarta ta zamani.
Darektar lamurran sadarwa na NELFUND, Oseyemi Oluwatuyi, ita ta bayyana hakan a, wani jawabin da aka rabawa manema labaru ranar Lahadi ta makon daya gabata.
- Kasar Sin Za Ta Dage Dakatar Da Shigo Da Waken Soya A Kan Kamfanonin Amurka Uku
- Kasar Sin Ta Musanta Zargin Da Wakilin Amurka Ya Yi Game Da Batun Sauyin Yanayi
Ta ce an cimma nasarar ne bayan shekara daya kacal da kaddamar da tsarin bada bashi ranar 24 ga Mayu, 2024, inda tace tsarin ba dalibai bashin karatu yana taimakawa, kuma al’umma suna ta yin maraba da shi.
Kamar yadda hukumar ta bayyana ta bada bashi Naira biliyan 116 ga daliban da suke karatu a Jami’oi, Kwalejin ilimi,da kuma Makarantun fasaha a Nijeriya, bashin dai kudin makaranta da kuma na alawus alawus domin tafiyar da rayuwa a makaranta.
A cikin bayanana, an ji Shugaban hukumar NELFUND, Akintunde Sawyerr, yana cewa ci gaban da aka samu ya nuna irin damuwar da Shugaban kasa Bola Tinubu ya ke dangane da ilimi mai zurfi.
“Lamarin daya kai miliyan daya na wadanda suka nemi a basu bashin karatu, lalle abin ya nuna a gaskiya matasa sun son su kyautata yadda rayuwarsu data wasu zata kasance a gaba, musamman ma yadda suka maida hankali wajen neman ilimi.
Ya ci gaba da bayanin “Wannan yana nunawa a fili yadda jagorancin na Shugaban kasa Bola Tinubu ya damu da lamarin ilimi domin shi ne ginshikin ci gaban al’umma kamar yadda ya ce,”.














