Hukumar Ba da Agajin Gaggawa ta Kasa (NEMA) a ranar Laraba ta bayar da tallafin kayayyakin agaji ga wadanda hare-haren ‘yan bindiga, da bala’in ambaliyar ruwa da kuma ‘yan gudun hijira ya shafa a Zamfara.
Darakta-Janar ta hukumar, Hajiya Zubaida Umar ce ta bayyana hakan a lokacin da take mika kayayyakin ga gwamnatin jihar a Gusau.
- Shirin NG-CARES: Gwamna Lawal Ya Tallafawa Mutane 44,000 Da Fiye Da Naira Biliyan 4
- Babu Wanda Zai Ci Nasara Daga Ayyukan Lalata Tsarin Samar Da Kayayyaki Na Duniya
Babban daraktar ta samu wakilcin shugaban ofishin ayyuka na hukumar da ke Sokoto, Mista Aliyu Kafindangi.
Hajiya Zubaida ta ce, shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya amince da raba tallafin ga al’ummomin da abin ya shafa domin rage musu radadi.
Da yake karbar kayayyakin, Gwamna Dauda Lawal, ya yabawa Gwamnatin Tarayya bisa wannan karamcin tare da bayar da tabbacin cewa, za a raba kayayyakin ga wadanda aka tsara bai wa.