Leadership News Hausa
No Result
View All Result
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
No Result
View All Result
Leadership News Hausa
No Result
View All Result

NEMA Ta Raba Kayan Abinci Ga ‘Yan Gudun Hijirar Jihar Neja

by
1 year ago
in LABARAI
1 min read
Hukumar NEMA Ta Bada Tallafin Kayayyaki Ga Gidaje 45,577 A Jihar Kogi
WhatsAppShare on FacebookShare on TwitterShare on Telegram
ADVERTISEMENT

Daga Mahdi M. Muhammad,

Hukumar bayar da agajin gaggawa ta kasa (NEMA), ta fara raba kayayyakin tallafi ga gidaje 24,925 na ‘yan gudun Hijira (IDP) da ‘yan bindiga suka addaba a kananan hukumomi 14 na jihar Neja.

An bayyana hakan ne a wata sanarwa da Manzo Ezekiel, shugaban sashen yada labarai da hulda da jama’a na hukumar a ranar Alhamis a Abuja.

Labarai Masu Nasaba

“Ina Cikin Wani Hali, An Kashe Matata Da Ciki Wata 9 Da Yara 4” —Mijin Matar Da IPOB Suka Kashe

An Karrama Buhari Da Lambar Yabo Kan Kwazonsa Wajen Yaki Da Cin Hanci Da Rashawa

Air Vice Marshal Muhammadu Muhammed (mai ritaya), Shugaban NEMA wanda Hajiya Zainab Saidu, Shugabar ofishin Minna na hukumar ta wakilta ta kaddamar da rabon kayayyakin a Kuta, karamar hukumar Shororo.

Sauran kananan hukumomin sun hada da, Rafi, Shiroro, Bosso, Munya, Paikoro, Mariga, Kontagora, Magama, Mashegu, Wushishi, Rijau, Borgu, Lapai da Labun.

A cewarsa, kayayyakin agajin sun samu amincewar shugaban kasa Muhammadu Buhari don tallafawa kokarin gwamnatin jihar Neja da sauran su don samar da agaji ga mutanen da abin ya shafa.

ADVERTISEMENT

Ya kara da cewa, bayan tantancewar hadin gwiwa da NEMA da gwamnatin jihar suka gudanar kwanan nan, an gano cewa ‘yan gudun hijirar na bukatar tallafin abinci.

“A kan wannan ne aka samu amincewar shugaban kasar da kuma abubuwan da ake bukata wadanda suka hada da buhunan shinkafa buhu 5, 412, kilo 5,412 na wake 10, lita 500 na man kayan gyada, katun 500 na kayan dandano da buhu 500 na gishiri ga masu amfani,” in ji shi.

Ya ci gaba da cewa, “za a rarraba kayayyakin ne kai tsaye ga mutanen da abin ya shafa a sansanonin da kuma wuraren da ke karbar bakuncin ta hanyar NEMA tare da hadin gwiwar jami’an hukumar ba da agajin gaggawa ta Jihar Neja.”

 

Like this:

Like Loading...
SendShareTweetShare
Previous Post

Sakon Sallah: Kuji Tsoron Allah Ku Guji Zalunci –Inji Sheikh Aminu Sha’aban

Next Post

An Cafke Jami’an EFCC 2 Na Bogi A Legas

Labarai Masu Nasaba

“Ina Cikin Wani Hali, An Kashe Matata Da Ciki Wata 9 Da Yara 4” —Mijin Matar Da IPOB Suka Kashe

“Ina Cikin Wani Hali, An Kashe Matata Da Ciki Wata 9 Da Yara 4” —Mijin Matar Da IPOB Suka Kashe

by Leadership Hausa
4 hours ago
0

...

An Karrama Buhari Da Lambar Yabo Kan Kwazonsa Wajen Yaki Da Cin Hanci Da Rashawa

An Karrama Buhari Da Lambar Yabo Kan Kwazonsa Wajen Yaki Da Cin Hanci Da Rashawa

by Muhammad Bashir
6 hours ago
0

...

IPOB Ta Yi Allah-Wadai Da Kisan Wata Mata Bahaushiya Da Yaranta 4 A Anambra

IPOB Ta Yi Allah-Wadai Da Kisan Wata Mata Bahaushiya Da Yaranta 4 A Anambra

by Muhammad Bashir
15 hours ago
0

...

Nijeriya Zata Ringa Kashe Miliyan 999 Kullum Wurin Ciyar Da ‘Yan Firamare Miliyan 10

Nijeriya Zata Ringa Kashe Miliyan 999 Kullum Wurin Ciyar Da ‘Yan Firamare Miliyan 10

by
16 hours ago
0

...

Next Post
Kashe

An Cafke Jami'an EFCC 2 Na Bogi A Legas

Domin bayar da talla ko neman ƙarin bayani a tuntuɓe mu a: +2348039216372

  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
Advertise with us | English Edition | Fashion Magazine | Business News

© 2022 Leadership Media Group .

No Result
View All Result
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU

© 2022 Leadership Media Group .

%d bloggers like this: