Hukumar Bayar da Agajin Gaggawa ta Kasa (NEMA), ta fara rabon kayayyakin tallafi ga mutanen da ambaliyar ruwa ta shafa a 2024 a unguwanni uku na Karamar Hukumar Kaduna ta Kudu.
Jami’in hukumar na yankin Arewa maso Yamma, Imam Garki, ya ce kayayyakin an kawo su ne don rage wahalhalun da mutanen ke fuskanta.
- An Kashe Mutum 50, An Sace 170 Cikin Wata 7 A Kaduna
- An Fara Watsa Shirin Zababbun Kalaman Da Shugaba Xi Jinping Ya Fi Kauna A Kasar Brazil
Wadanda suka amfana daga unguwannin Tudun Nupawa, Tudun Wada, da Anguwar Mu’azu sun karbi kayan abinci irin su shinkafa, masara, man girki, da kuma kayayyakin gine-gine kamar siminti da sauransu.
Hakazalika, an ba su tufafi da tawul.
Garki, ya ce tallafin ba zai magance matsalolin gaba daya ba, amma zai rage tasirin abin da suka haifar.
Shugabannin al’umma da Dan Majalisa Hussaini Ahmed, sun yaba wa NEMA kan wannan tallafin da ya zo cikin lokaci.