Umar A Hunkuyi" />

Neman Shugabancin Majalisar Dattawa Ya Dauki Sabon Salo Yayin Da Goje Ya Janye Takararsa

Bayan ganawarsu da Shugaban kasa Muhammadu Buhari, a ranar Alhamis, Sanata Danjuma Goje, ya shelanta janyewarsa daga takarar shugabancin majalisar ta Dattijai.

Shugaban kasan ya kuma gana ne da mutane biyun da suke a kan gaba wajen takaran shugabancin majalisar ta 9.

Shugaban masu rinjaye na majalisar, Sanata Ahmed Lawan, da kuma Sanata Danjuma Goje, wadanda su ne a sahun gaba cikin masu neman kujerar shugabancin majalisar ta Dattawa a karkashin jam’iyyar APC, sun gana ne da Shugaban kasan a fadar gwamnati da ke Abuja.

Har-ila-yau, a cikin ganawar tasu akwai Gwamnan Jihar Kaduna, Malam Nasir El-Rufai. Ganawar dai ta zo ce ‘yan kwanaki kadan kafin kaddamar da zaman majalisar ta tara.

A ranar Talata ce ake sa ran kaddamar da zaman majalisar ta Tara. Wakilinmu ya bamu labarin cewa, janyewar da Goje ya yi daga takarar yanzu ta sa kallo ya koma sama, bisa irin sabon salon gwagwamaryar kujerar da za a yi a tsakanin Sanata Ali Ndume da kuma bangaren su Lawan da Goje.

Hausawa dai na cewa ba a san maci tuwo ba, sai miya ta kare.

Exit mobile version