Neman Zaman Lafiya: Gwamnonin Arewa Sun Ziyarci Binuwai

Tawagar wasu daga gwamnonin arewa sun kai ziyarar ta’aziyya zuwa Jihar Binuwai, sakamakon rikice-rikicen da suka ki, suka ki cinye wa.

A ziyarar, gwamnonin sun nuna alhininsu dangane da rikicin dake faruwa a jihar.

Tawagar gwamnonin sun kai wannan ziyarar Jihar Binuwai da nufin jajanta wa gwamnan jihar, Samuel Ortom da sauran al’ummar jihar bisa ibtila’in da ya afka musu na rikici da kashe-kashe.

Gwamnonin da suka kai wannan ziyarar sun hada da Gwamnan Jihar Borno, Kashim Shettima, gwamnan Jigawa, Muhammad Badaru Abubakar, gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello, Gwamnan Kaduna Malam Nasiru El-Rufai, sai kuma mataimakiyar gwamnan jihar Osun.

Gwanonin sun isa jihar ne a a jiya, inda suka samu ganawa da gwamnan jihar Samuel Ortom, manyan jami’an gwamnatin da kuma jama’an jihar, inda suka mika sakon uwar kungiyarsu ga jama’an, tare da nuna alhinin halin da suka shiga. Sun kuma bukaci al’umman Jihar da su rungumi akidar zaman lafiya da juna.

Jihar Binuwai na daya daga cikin jihohin Nijeriya dake fuskantar barazanar tsaro sakamakon rikici dake faruwa tsakanin Makiyaya da Manoma, wanda yayi sanadiyyar mutuwar mutane da dama, sauran jihohin da lamarin yayi kamari sun hada da Taraba, Kaduna da Nassarawa.

Wannan ziyarar dai ta biyo bayan kurarin da Gwamnan Jihar Binuwai, Samuel Ortom yayi a kwanakin bayan na cewa zai fice daga kungiyar gwamnonin Arewa, sakamakon rashin goya masa baya da gwamnonin suka yi dangane da abin da ke faruwa a Jiharsa.

 

 

 

 

Exit mobile version