Dan wasan kungiyar kwallon kafa ta Al Hilal Neymar Jr ya buga wasan farko na gasar Saudi Pro League tare da sabuwar kungiyarsa ta Al Hilal.
Inda ya fara da kafar dama yayin da kungiyarsa ta lallasa abokiyar karawarta Al Riyadh da ci 6-1 a babban birnin Saudiyya.
- Neymar Ya Zarce Pele A Matsayin Wanda Yafi Zurawa Kasar Brazil Kwallaye
- Neymar Jr Ya Koma Kungiyar Al Hilal Ta Kasar Saudiya Da Taka Leda
Dan kasar ta Brazil Neymar Jr wanda ya koma kungiyar a bana bayan barin tsohuwar kungiyarsa ta Paris Saint Germain ta kasar Faransa.
Ya fara wasansa na farko a Saudiya bayan dawowa hutun rabin lokaci.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp