Dan wasan gaba na kasar Brazil Neymar Jr wanda ya ke buga kwallo a kungiyar Al Hilal dake buga babbar gasar kasar Saudiya ya samu rauni a wasan da kungiyar ta buga a rukunin B na gasar AFC Champions League tsakaninta da Al-Ain, hakan ya sa likitoci suka bayar da shawarar ya shafe tsawon mako biyu kafin ya murmure daga jinya.
Neymar zai yi jinyar akalla makonni biyu bayan samun rauni a tsoka a wasansa na biyu da ya yi bayan kwashe tsawon lokaci ba tare da buga wata gasar kwallon kafa ba in ji kocin kulob din Al Hilal Jorge Jesus.
- Na Fi Jin Dadin Rubutu In Na Gaji Tibis – Maryam Faruk
- EFCC Ta Gurfanar Da Tsofaffin Gwamnoni Da Tsofaffin Ministoci, Bayan Kwato Kadarorin Biliyoyin Naira A Kasashen Waje
Tauraron dan wasan na Brazil ya buga mintuna 26 kacal a matsayin wanda ya maye gurbin Al Hamdan bayan dawowa daga hutun rabin lokaci kafin ya ji rauni hakan ya sa koci Jorge Jesus ya cire shi a wasan da suka doke Esteghlal da ci 3-0 a gasar cin kofin zakarun kasashen yankin Asiya na ranar Litinin.
Neymar, mai shekara 32, wanda ya koma Al Hilal daga Paris Saint-Germain a kwantiragi mai tsoka a shekarar 2023, ya shafe fiye da shekara guda yana jinya har zuwa watan da ya gabata bayan tiyatar da aka yi masa a gwiwarsa ta dama, likitoci sun tabbatar da cewar Neymar ya murmure daga tiyatar da aka yi mashi amma dai dole ya dinga samun yan kananan matsaloli duba da dadewar da ya yi bai buga kwallo ba.
Al Hilal, mai rike da kofin na Saudiyya, ba ta yi wa Neymar rajista ba a gasar cin kofin Saudi Pro League da aka fara a watan jiya, amma tsohon dan wasan na Barcelona ya fi kowane dan wasa samun albashi a kungiyar inda yake karbar albashin kusan Yuro miliyan 100 (Dala miliyan 112) a shekara.