MARYAMA NASIR matashiya ce wacce ta yi tsayin daka wajen ganin ta rufa wa kanta asiri gami da dogaro da kanta ta hanyar kasuwanci, ta bayyana wa shafin Adon Gari bayanain yadda ta rungumi kasuwanci da irin ci gaban da ta samu har ma da kalubalen da ke fuskanta. Inda ta ce mahaifanta sun tallafa mata sosai da karfinsu wajen ganin wannan kasuwanci nata ya tsaya da kafarsa. Ga tattaunawar kamar haka:
Da fari za mu so sanin cikakken sunanki da tarihinki?
Da farko sunana Maryam Nasir, an haife ni a garin Kano a Unguwar Tarauni. Na yi firamare a Makama Acadamy, na yi Sikandire a Hayatudeen Islam.
Shin Maryam matar aure ce?
Eh ni matar aure ce ina da da daya
Shin ‘yar kasuwa ce ke ko kuma ma’aikaciya?
A’a ni ba ma’aikaciya ba ce, ni ‘yar kasuwace ina sayar da Abaya da su leshi, sannan ina da shagon kwalliya.
Wane irin kasuwanci kike yi?
Kamar yadda na gaya miki a baya ina sai da abubuwa da dama sannan kuma ina da shagon kwalliya (Makeup).
Shin me kasuwancin naki ya kunsa? Ma’ana kamar me da me kike sarrafawa?
Kasuwancina ya kunshi abubuwa da dama ina harkar kayan maza da na mata kamar atamfa leshi shadda da abaya.
Me ya ja hankalinki har kika shiga wannan kasuwancin?
Gaskiya tun ina yarinya zan ce kamar tun ina JSS 1 nake sana’a zan iya cewa gaskiya son sana’a a cikin jinina yake. Saboda ni mutum ce mai son na ga na rufa wa kaina asiri ba na son na ga na nemi abu na rasa kuma ni bana son yin roko shi ya sa nake da zummar yin sana’a ita ce kadai hanyar da mutun zai nemi kudinsa, sannan kuma ka rufa wa kanka asiri har da wani ma, ba tare da ka yi roko ba, shima wanda yake tare da kai zai ji dadi koda ko ya dauke maka daweniyarka amma ana tuna gaba.
Baki fada mana matakin karatunki ba?
To ni a gaskiya ban yi karatu mai zurfi ba, iyaka ta sakandire na gama ban ci gaba ba
Wane irin kalubale kika taba fuskanta a cikin sana’arki?
To a gaskiya na sha fuskantar kalubale da yawan gaske, amma Alhamdu lillah sanadiyyar addu’ar iyaye komai ya zama tarihi in sha Allahu amma an wahala sai dai na ce Alhamdulillah.
Zuwa yanzu wadanne irin nasarori kika cimma?
To Alhamdulillah a gaskiya na samu nasarori da yawan gaske sai de na ce
Alhamdulillah, daga cikin nasarar da na samu gashi na mallaki shagon kaina, sannan ina taimakon kaina har da na kasa da ni, ina da abin hannuna to a gaskiya wannan ba karamar nasara bace sai dai na gode wa Allah.
Wanne abu ne ya fi faranta miki rai game da sana’arki?
To babu abin da yake faranta min rai game da sana’ata kamar mutum ya sayi kayana ya nuna min ya ji dadinsu har gobe shima ya kawo wani, gaskiya wannan abin ba karamin dadi nake ji ba na farantawa masu sayen kayana rai da abin da suke so, su same shi yadda suka yi tsammani ko kuma ya fi haka ina jin dadi haka sosai gaskiya.
Ta wacce hanya kike bi wajen tallata sana’arki?
Ina tallata kayana ta soshiyal Midiya, sannan kuma da mutane na har ma daga wasu mutanena ina samun masu sayen kayana Alhamdulillah.
Dame kike so mutane su rika tunawa dake?
Ina so mutane su rika tunawa da ni da gaskiyata, sannan kuma da rikon amana, da kuma yadda nake sayarda kayana, idan ka turo kudinka babu wata-wata za a tura maka kayanka dama duk abin da nake saidawa in zan yi tallan sa ko kuma na ce idan na karbi kudinsa to in sha Allahu wannan abin akwai shi a kasa ba wai babu ba, sannan zan je nemo shi a a dama na saro kayana, to ina so mutane su rika tunawa da ni da haka.
Ga sana’a ga kuma hidimomin gida, shin ta yaya kike samun damar gudanar da hutunki?
To gaskiya ina samon hutawa saboda sana’a ta ba wai ta takura bace da har za ta hana ni hutawa, kin ga shago akwai ma’aikata ba wai ni kadai ce ba to gaskiya ba ni da wata matsala ta nan.
Wace irin addu’a ce idan aka yi miki kike jin dadi?
Addu’ar da ake min nake jin dadi ba ta wuce a yi wa mahaifana ba ko dana.
Wane irin goyon baya kike samu daga wajen iyaye da ‘yan uwanki?
Gaskiya na samu dukkan goyon baya daga wurin mijina da mahaifana sun tallafa min sosai da dukkan karfinsu
kawaye fa?
Gaskiya ba ni da kawa a duniya da ta wuce mahaifiyata, duk wata shawarata ita ce.
Me kika fi so cikin kayan sawa da kayan kwalliya?
Gaskiya ina son Abaya itace kayan da na fi sawa. Kwalliya kuma ba sosai ba gaskiya.
A karshe wace irin shawara za ki ba ‘yan uwanki mata?
Shawara da zan ba wa ‘yan uwana mata su dage da sana’a sannan kuma duk kalubalen da zai tunkare su a sana’a kar su yi kokarin ja da baya su dage har su kai ga cin nasara, ina so su sa a ransu komai ya yi farko zai yi karshe. Sannan kuma bayan wahala sai dadi dama duk wani abu na rayuwa sai an wahala ake samu.