Connect with us

ADABI

Ni Na Fara Wallafa Littafin Tarihin Shata A Duniya (II)

Published

on

Ci gaba daga makon da ya gabata

To, a unguwar Takuntawa inda ya ke da zama sai aka kai ni wajen abokan huldar sa, to su su ka kai ni wajen sa a Bompai. Sai na tarar suna da wata kungiya mai suna Young Writers Club (YWC) Kano, wadda Kabirun ma mamba ne. To nan su ka rike ni na yi kwanaki a wajen su, su ka yi mani abin arziki, nan kuma na rika kwana wajen su. Kuma su ka bani fam na cika na zama dan kungiya. Ina tuna cikin su akwai Suleiman Gezawa, Rabi’u Kura, Rabi’u Mohammed, Mohammed Garzali, da sauransu. A cikin shirye-shiryen kungiyar ana rubuta tarihin mutanen da su ka shahara ko na garuruwa. To sai su ka bani shawara mi za ya hana in tafi Funtuwa in nemo izinin rubuta tarihin Shata daga wajen sa ? Tunda dama sun yi tunanin hakan tun kafin in bakunce su. Sai na amince. Na tafi Funtuwa, na yi sa’a na samu Shata a gida, na bashi labarin abinda ake ciki da kudurin wannan kungiya, da abin da ta sanya ni in yi mata. Ya yi murna. Har na ce masa : ‘sun ce ka fadi mani ranar da ka ke a gari, don mu zo tare da su’. Ba zan manta ba har ya kama fada ya na ce mani ‘ai yanzu na girma, na daina yawon zage, bare a ce a za a zo ba a same ni ba, saidai fa ko in kun ji ana wani buki a Rediyo, watakila zan je, to sai ku dakata sai randa ku ka ji ba a yin wata sabga ko nadin sarauta’. Mu ka rabu a haka. Na koma Kano na shaida masu. Su ka bani dama da in rubuta littafin. Na fara rubutu, wanda ya kai ni har cikin 1994 (bayan shekara 2 kenan) Na kammala. Sai mu ka kai littafin ga Ahmed Mohammed wani mai kafanin buga littattafai a Gidan Goldie kusa da Singer, Kano. Ana ta cuku-cukun ya za a yi a samu kudi a buga shi, sai na tafi bautar kasa a Legas. Ran da ma zani tafi, na biya ta Funtuwa na yi bankwana da Shata (ran Lahadi 13/11/1994) har ma na bashi kofin littafin, ya amsa ya rika ya duba. Har ya na cewa ‘yanzu nan wannan duk aikin tarihi na ne? Na ce masa ‘e’. Ya yi fatar Allah sa albarka. Sannan ya ce idan na dawo daga Ikko za mu zauna. Ya kuma lissafa mani wasu a Legas da in na je in yi ma intabiyu, mutanen sa kamar su Alhaji Na’Allah Dan Ibrahim da Alhaji Salmanu Agege, shugaban ‘Yan Daudu na Afirka, da sauran su. Kuma na yi hakan.

Shirya Littafin Shata Ikon Allah

Na dawo daga bautar kasa cikin 1995. Sai kuma abokan aiki na na Kano su ka nuna gazawa ga buga littafi na jan kafa. Waje daya kuma na samu labarin Ibrahim Sheme daga Ya’u Wazirin Shata da wani abokina Kabir Dan’azumi Kankara wanda mazaunin Kaduna ne, bil hasali ma gida daya su ke zaune da Sheme din a unguwar Badikko. Kafin Ya’u waziri ya kara tunkara ta da maganar Sheme, sai kwaram rannan Shata ya yi ma ni bayanin sa. Ya ce mani na san shi? Na ce masa ‘ban san shi ba, ba mu taba haduwa ba’. Shata ya ce mani ya kamata mu hadu, abinda ba ni da shi ya taimaka mani da shi, shi ma abinda ba ya da shi, da ni ni ke da shi sai in bashi’.  Amma bai nuna ya na so mu hade ba, amma ni a fahimta ta haka Shata ke nufi.  A waje daya Ibrahim Malumfashi (wanda ya zama Farfesan Hausa daga bisani) ma ya taba yi mani maganar sa, amma ba shi ya kai ni wurin sa ba.  Ni na kai kai na wurin Sheme a gidan san a Badikko din nan da dare, ina kuma zaton cikin 1995 din ne, don lokacin ban ma gama bautar kasa ba.  Sheme ya yi murna da gani na, cewa ya dade ya na jin labari na amma sai rannan mu ka hadu. Ya zaunar da ni, ya dauko mani aikin san a littafin Shata na gani, na kuma yaba.  Tun daga rannan bamu kara haduwa ba sai cikin 1997 da na koma Kwalejin Ilimin Kimiyya ta Kaduna da aiki. Ya taba samu na a ofis, ya nunaya kamata idan zamu hade ayyukan mu wuri daya mu yi haka, idan kuma ba mu yi to kowa ya kama gabansa. Matata Habiba (‘yar mutanen Mangu)ta na sheda cewa Sheme, ban da ofis (tunda wannan ba ta gani ba) ya taba zuwa gida na a nan Kwanar PRP kusa da Angwan Sanusi duk akan zancen yiwuwar hadewar mu. Da, da farko Sheme na zawarci na amma na so in noke saboda halin rayuwa a gaba, amma sai matata ta nuna tunda ya nuna yana so mu hade in dauki aiki na in bashi, ta ce ta tabbata a gaba abin alheri za ya zama. Ta kuma tabbatar mani da cewa duk da ya ke ba ta taba ma ganin sa ba, ta san ba za ya cuce ni ba. Na rantse da girman Allah abin da ya faru kenan. Sai na aminta. Ran wata Asabar da safe Ibrahim Sheme ya zo waje na ya ce in dauko masa littafi na ya gani. Ba musu na shiga na dauko littafi gaba daya na bashi, don ni ba na iya tsallake maganar matata. Na yarda da ita. Mu na nan mu na nan, sai ya tura ni in yi intabiyu da wasu mutanen Shata, don shi ayyukan ofis sun sha masa kai. Kuma ina ta yi masa biyayya saboda ko ba komi akwai tazarar shekaru kimanin 2 ko 3 ma kuma ya na gabana a makaranta. Gashi a lokacin ya na ‘sabon-huji’, ya fito fes, ya kammala karatun Digiri na Biyu daga Ingila, ya na ta bani sha’awa. Inda duk ya tura ni ba gardama sai in tafi, watau a nan Kaduna. Sannan kuma na kan dauke shi in kaishi ga wasu da Shatan ya yi ma waka da shi bai ma san su ba, misali: Malam Na Gwandu mai nama, wanda ta hanyar Ahmadu Doka na san a Kaduna ya ke da zama. Sannan na dauke shi na kaishi ga Hauwa ‘yar Bori matar marigayi Sarkin Bori Sule a Titin Bashama Tudun Wada Kaduna. Dole ne in fi Ibrahim Sheme sanin mutanen da Shata ya wake sabili da a kullum ina tare da Ahmadu Doka (unguwa daya mu ke zaune) da sauran makada da mawaka da su ka sha yin kwaramniya da Shatan, su ke bayyana mani mutanen Shatan. Ni da Doka, kuluyaumin ba mu da wani labari sai na Shatan.

Cikin 1998 sai Sheme ya tafi Funtuwa, ya tarar Shata ya kwanta asibiti a Kano. A nan ya samu labarin wasu ‘yan Kano su 2 su na rubuta tarihin sa daga bakin Shatan, don sun ma same shi aasibiti sun nuna masa aikin da su ka yi. Saidai su Sarkin Daura ya sanya su. Saboda haka Shata ya ce ma Sheme ya tafi Kano ya nemo su ya ce su zo Funtuwa ya na kiran su, don ya sanya su hade da mu. Amma Shata ya yi ma Sheme kashedin kada ya bayyana masu cewa bukatar sa a hade. Sheme ya dawo Kaduna ya same ni gidan marigayi Adamu Yusuf BBC ya bayyana mani abinda ke faruwa. Har na bata rai sai ya bani hakuri y ace haka Allah Ya so kuma mu yi fatan Allah sa abin ya zama alheri. Mu ka sa ranar tafiya Funtuwa, watau Asabar mai zuwa ta ran 19/9/1998. Tun ran Juma’a Sheme ya dauke ni, tare da wani abokinsa Aimana Datti Usman mu ka tafi mu ka kwana Funtuwa. Wanshekare da safe mu ka hadu da baki daga Kano a gaban Shata. Nan da nan Shata ya nuna da za a hade da ya fi, amma mu je mu yi shawara. Mu ka fito garejin motar sa mu ka yanke cewa mu 4 mu zama daya ga wannan tafiya. Mu ka koma mu ka shaida masa.

Amma cikin ikon Allah sai Allah Ya mantar da Shata ya tuna ma Sheme da sauran bakin nan wancan zancen littafin sa da na ke yi da kungiyar YWC ta Kano su ka sanya ni. Ni kuma, saboda kawaici sai Allah Ya rufe mani baki, saboda ma ina ganin ga wani sabon shafi an bude, to mi za ya sanya in kawo zancen abin da ma ya wuce?

Mu kwana nan, za mu dora a gaba insha Allahu.
Advertisement

labarai