Daga El-Zaharadeen Umar, Katsina
Wani Mutum mai suna Akilu Sa’idu wanda yanzu haka ya ke hannun jami’an ‘yan sanda ya tabbatar masu da cewa shi ne, kansa ya kashe diyar kishiyar matarsa mai suna Saratu Yahuza.
Al’amarin dai ya faru ne, a cikin wani gina da ba a kammala ba, da ke garin ‘Yankara da ke karamar hukumar Faskari a jihar Katsina. Ya yi amfani da karfin tuwo wajen murde mata wuya wanda hakan ya yi sanadiyar mutuwarta.
Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sanda ta jihar Katsina, DSP Gambo Isah ya tabbatar da faruwan lamarin, inda ya ce haka ta faru ne dalilin bacewar hankalin wanda ake zargin da aikata laifin.
DSP Gambo Isah Ya bayyana cewa bayan faruwar lamarin an dauki gawar Yarinyar zuwa babban asibitin Funtua inda likita ya tabbatar da rasuwar ta.
Tunda farko an kai rahoton lamarin ne zuwa ga ofishin ‘yan sanda na karamar hukumar Faskari wanda kuma mahaifin yarinyar mai suna Yahuza Yakubu ya kai, yanzu haka dai an maida wannan batu zuwa shelkwatar ‘yan sanda da ke Katsina domin cigaba da bincike da daukar mataki na gaba.