Gwamnatin Jamhuriyar Nijar ta sanar da ficewarta daga ƙungiyar ƙasashe masu amfani da harshen Faransanci, International Organisation of the Francophonie (OIF).
A wata sanarwa da gwamnatin Nijar ta aike wa ofisoshin jakadancinta a duniya a ranar Litinin, 17 ga watan Maris, da kuma sa hannun babban sakataren gwamnati, Laouali Labo, ta bayyana cewa:
- Fa’ida Daga Tafsirin Alƙur’ani Na Ibnu Juzai [10]
- Atisayen Soji A Mashigin Tekun Taiwan Babban Gargadi Ne Ga ‘Yan Awaren Taiwan
“Jamhuriyar Nijar ta yanke shawarar janyewa daga ƙungiyar ƙasashen duniya masu amfani da harshen Faransanci.”
Sanarwar ta kuma umarci jakadun ƙasar da su isar da wannan mataki ga ƙasashen da suke.
OIF ƙungiya ce da ke da mambobi 93 daga faɗin duniya, wadda aka kafa domin bunƙasa harshen Faransanci, zaman lafiya, da ci gaban tattalin arziƙi da ilimi.
Tun bayan juyin mulkin da ya kifar da tsohon shugaban ƙasar, Mohammed Bazoum, Nijar na ci gaba da janye jikinta daga ƙungiyoyin yammacin duniya.
A baya-bayan nan ma, tare da Mali da Burkin Faso, ƙasar ta fice daga ƙungiyar ECOWAS.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp