Daga CRI Hausa
A jiya Lahadi Jamhuriyar Nijer ta karbi gudummawar alluran riga-kafin cutar COVID-19 daga kasar Sin wanda tuni sun riga sun isa Niamey, babban birnin kasar.
Shugaban kasar Nijer Mahamadou Issoufou, da firaministan kasar ta Nijer Brigi Rafini, da ministan lafiyar kasar Ahmed Boto, gami da jakadan kasar Sin a Jamhuriyar Nijer Zhang Lijun, sun halarci bikin mika alluran riga-kafin wanda ya gudana a filin jirgin saman kasar.
Shugaba Issoufou, ya bukaci jakadan kasar Sin da ya mika sakon godiyarsa ga gwamnatin kasar Sin da al’ummar Sinawa bisa wannan tallafi.
Haka zalika, shugaban kasar ta Nijer ya taya murnar samun kakkarfar dangantaka da hadin gwiwa a tsakanin kasar Sin da Nijer, ya kara da cewa, a wannan rana sun karbi gudummawar alluran riga-kafi daga gwamnatin Sin domin yaki da annobar COVID-19. Ya ce zai yi amfani da wannan damar domin taya murnar kyakkyawar dangantaka dake cigaba wanzuwa a tsakanin Nijer da kasar Sin.
A cewar Shugaba Issoufou, bayan samun wannan gudummawa, Nijer za ta fara aikin riga-kafin cutar COVID-19 a ranar Asabar mai zuwa, inda za a bada fifiko ga ma’aikatan lafiya, da mutane masu fama da wasu cutuka da kuma masu yawan shekaru, da jami’an hukumomin tsaro.
Kawo yanzu, Nijer tana da jimillar mutane 4918 da aka tabbatar sun kamu da cutar COVID-19, yayin da cutar ta yi sanadiyyar mutuwar mutane 185, kana mutane 4538 sun warke daga cutar.(Ahmad Fagam daga sashen Hausa na CRI)