Gwamnatin tarayya ta sanar da kulla wata yarjejeniyar tsaro tsakaninta da Japan wadda za ta bai wa kasashen biyu damar yin hadin gwiwa a wajen yaki da matsalolin tsaron da suka addabi kasashen yankin Sahel.
Ma’aikatar harkokin waje ce ta sanar da kulla yarjejeniyar, inda ta ce aikin yaki da matsalolin tsaron na hadaka tsakaninta da Japan zai shafi kasashen da suka kunshi Nijar da Chadi da Sudan da Senegal baya ga Sudan ta Kudu da kuma Jamhuriyar Tsakiyar Afrika sai Mali da Burkina Faso tare da Mauritaniya.
- Kwale-kwale Ya Yi Ajalin Dalibai 2 A Kano
- Ranar Ma’aikata: Bayan Cike Giɓin Albashin Da Muka Gada, Za Mu Ci Gaba Da Inganta Walwalar Ma’aikata – Gwamnan Zamfara
Wata sanarwar hadaka tsakanin Japan da Najeriya wadda ma’aikatar wajen Na
Nijeriyar ta fitar bayan ganawar kwanaki biyu tsakanin wakilan kasashen.
Ta ruwaito ministan harkokin wajen Nijeriya, Yusuf Tuggar na cewa kasashen biyu za su yi aiki ne don warware tushen matsalolin da suka haddasa rashin tsaro a kasashe yankin Sahel da ma ta’addancin kungiyar Boko Haram da ya wargaza tsaron yankin Arewa Maso Gabas.
A bangare guda ministar harkokin wajen Japan, Misis Kamikawa Yoko, ta bayyana cewa kasashen biyu sun aminta da hada karfi don magance matsalolin tsaron da ke barazana ga kasashen yankin Sahel, kuma ko shakka babu kasarta za ta bayar da dukkanin tallafin da ake bukata wajen samar da zaman lafiya a kasashen.
Ta kuma bayar da tabbacin zuba jari a wasu jihohi na Nijeriya baya ga bayar da gudunmawa wajen tabbatar da ‘yancin mata wayar da kai da kuma habaka tattalin arziki.
Bayanai na nuna cewa Japan na shirin fadada bangarorin kera-keran fasahar zamani a sassan Nijeriya.