Connect with us

NOMA

Nijeriya Na Bukatar Taraktocin Noma 750,000

Published

on

Kwarru a fannin aikin noma a kasar nan sun sanar da cewa, Nijeriya na bukatar Taraktocin noma a yanzu guda 750,000 don biyan bukatar Manoman dake a kasar nan.

Nijeriya dai ba ta kera Taraktocin noma tana shigo dasu ne kawai cikin kasar nan.

Amma akwai kanan Taraktocin noma da Cibiyar yin noma da kayan noma na zamani ta kasa NCAM dake a garin Ilorin a jihar Kwara take sarrafawa.

Har ila yau, gwamnatin bata da kuma bayar da wani rangwame ga Manoman dake a karkara don su samar da amfanin gona mai yawa a kasar nan.

Wasu daga cikin Manoman sun bayyana cewa, za’a barsu a baya wajen yin nomad a kayan aikin noma na zamani, in har gwamnatin bata bayar da taimakon da ya kamata ba, musamman don a daukaka fannin samar da kayan aikin noma na zamani a kasar nan.

Shugaban kungiyar masu noma Tumatir na kasa Alhaji Abdullahi Ringim NTGPAN ya shawarci Gwamnatin Tarayya data fito da tsarin day a kamata yadda Manoman kasar nan zasu daina yin aikin gona da tsari na al’ada da aka saba dashi a kasar nan.

Ya yi nuni da cewa, an jima a Nijeriya ana yin hada Taraktocin noma, inda kusan aka shafe shekaru da dama, inda ya yi nuni da cewa, mun tsallaka daga Fartanyu zuwa Taraktocin noma amma kasar China ita kuma ta tsallaka daga yin amfani da Fartanyu zuwa yin amfani da Taraktocin noma na hannu.

A cewarsa, Nijeriya ta na da kasar fadin noma mai giraman gaske, inda mafi yawancin Manoman kasar suke da daga kadada daya zuwa kadada biyar.

Shugaban kungiyar masu noma Tumatir na kasa Alhaji Abdullahi Ringim NTGPAN kasashen dake a kasar waje suna baiwa kasashen kwarin gwaiwa sayen Taraktocin noman da suka kera.

A cewar Shugaban kungiyar masu noma Tumatir na kasa Alhaji Abdullahi Ringim NTGPAN, dukkan wadannan shekarun da aka shafe, kasashen basu zo sun koyar fasaha kan yadda za’a kera Taraktocin noma ba a Nijeriya.

Shugaban kungiyar masu noma Tumatir na kasa Alhaji Abdullahi Ringim NTGPAN baza ci gaba da dogara ana shigo da Taraktocin noma da kuma hada su cikin kasar nan ba.

Alhaji Abdullahi Ringim ya sanar da cewa hakan ne ya sanya ake baiwa mutane kwarin gwaiw dasu fara kera Taraktocin noma a kasar nan, inda ya ya sanar da cewa, akwai bukatar Gwamnatin Tarayya ta samar da wani shiri, inda nan da shekaru masu zuwa, za’a fara kera Taraktocin noma a kasar nan.

Shugaban kungiyar masu noma Tumatir na kasa Alhaji Abdullahi Ringim NTGPAN ya yi nuni da cewa, akwai bukatar mu dinga bai wa makeran dake a cikin kasar nan, musamman gannin yadda yan Nijeriya sukafi raja’a akan kayan da aka sarrafa a kasar waje aka kuma shigo dasu cikin kasar nan.

Da ya ke buga misali Shugaban kungiyar masu noma Tumatir na kasa Alhaji Abdullahi Ringim (NTGPAN) ya ci gaba da cewa, gwamnatocin Arewacin Nijeriya sun tsallake daga yin amfani da Fartanya zuwa yin noma da Shanu.

Har ila yau, a wani bincike da Cibiyar gudanar da bincike kan aikin noma ta kasa da kasa (IFPRI) Gwamnatin Tarayya ta yi kokarin magance matsalar maganar Taraktocin noma, amma har yanzu kwalliya bata biya kudin sabulu ba.

A yanzu kowa ya sani cewa, Gwamnatin tan a yin hayar Taraktocin noma, inda hukumomin gwamnatin suke rabar dasu akan farashi mai sauki ga manoman da suke da bukatar yin noma da su.

Wannan tsari dai bai dace ba domin Manoman da ake zabowa don su amfana, basu san yadda ake yin amfani da Taraktocin noman ba.

Gwamnatin Tarayya ta lura da hakan, inda ta janye shirin na rabar da Taraktocin noman akan farashi mai sauki a karkashin ajandar aikin noma na Gwamnatin Tarayya ATA.

Sai dai kuma Gwamnatin Tarayyar ta ci gaba da bayar da rage farashin na Taraktocin noman mafi yawanci ga kananan manoman dake kasar nan.

Bugu da kari, binciken ya kuma nuna cewa, samar da ranwamen bai kai yadda ake bukata ba domin baya warkar da komai kan matsalar.

Har ila yau, binciken ya kuma nuna cewa, yawan yian amfani da Taraktocin noma a kasar nan a bisa gajeren zango ya danganta ne kan irin tsarin da aka samar wanda ya dace da sauransu.

A karshe binciken ya sanar da cewa, rashin zuba jari mai yawa kan yin bincike a fannin noma a kasar nan, musamman noman rani hakan yana dakle habara fannin a kasar nan, inda hakan ya sanya ake shigon da abinci daga wasu kasashen dake ketare.
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: