• English
  • Business News
Saturday, November 1, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Nijeriya Na Da Dimbin Dukiyar Da Tinubu Zai Rika Tafiye-tafiye Zuwa Kasashen Waje – Minista

by Khalid Idris Doya and Sulaiman
9 months ago
Minista

Ministan kula da harkokin kasashen waje, Ambasada Yusuf Tuggar ya ce, Shugaban kasa Bola Tinubu na bukatar karin yin tafiye-tafiye zuwa kasashen duniya, sannan kuma Nijeriya na da dimbin dukiya.

Ministan ya ce a halin da ake ciki ma, tafiye-tafiyen da Shugaban Tinubu ya yi sun kasa domin bai ma yi tafiye-tafiyen da suke gabansa ba, domin kuwa yana bukatar ganawa da kuma tattaunawa da sauran shugabannin kasashen duniya.

  • Ana ɗar ɗar Kan Mutuwar Sojoji Bayan Da Tirela Ta Kwace A Legas
  • Fatara Da Talauci Na Yi Wa ‘Yan Nijeriya Miliyan 13 Barazanar Fadawa Kangin Talauci A 2025 — Rahoto

Wasu ‘yan Nijeriya na adawa da kuma kokawa kan yadda Tinubu ya dukufa yin tafiye-tafiye daga wannan kasar zuwa wancan, da ke janyo asarar makuden kudaden sufuri dukka da sunan nemo masu zuba hannun jari a Nijeriya.

Zuwa watan Mayun 2024, Tinuhu ya shafe kwanaki 96 a kasashen waje tun bayan da aka rantsar da shi a kan mulki, inda ya ziyarci wasu kasashe fiye da daya.

Tinubu dai ya ziyarci kasar Faransa, Ingila, Guinea Bissau, Kenya, jamhuriyar Benin, India, Hadaddiyar Daular Larabawa, Amurka, Jamani, Ethiopia, Senegal, Katar, da kuma Netherlands.

LABARAI MASU NASABA

Yadda Gwamnatin Tarayya Ta Dakile Yaɗuwar Ɓarkewar Cutar Dabbobi A Jihar Jigawa

Jerin Gwarazan Taurarinmu

Da yake magana ta cikin shirin siyasa na talabijin Channels, ministan ya ce, shugaban kasa bai yi wasu tafiye-tafiyen da suka isa ba.

“Har yanzu wannan gwamnatin sabuwa ce. An rantsar da shi a 2023. Ta fuskancin duniya har yanzu shi sabon shugaban kasa ne. Yana bukatar tattaunawa da ganawa da takwarorinsa domin gina alaka mai kyau a tsakaninsu, sannan kuna iya ganin amfanun irin wadannan tafiye-tafiyen.

“Za ka sake tafiya ka samu zuba jari na dala biliyan 2 kamar yadda ya yi a Brazil. A zahiri, ba mu ma yi tafiye-tafiyen da suka isa ba. Ina ba da shawarar mu sake yin wasu karin tafiye-tafiyen.

“Nijeriya tana da dinbin dukiya. Nawa ne tafiyar zai lakume idan aka kwatanta da amfanin da hakan zai samar. Sannan, yanzu nawa ne ma kudin idan ka kwatanta da abubuwan da shugaban kasa ya riga ya shawo kansu.

“Nawa muke barnatarwa a tallafin mai, wutar lantarki da sauran tallafi,” ministan ya tambaya.

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

Musabbabin Hana Sule Lamido Fom Ɗin Takarar Shugabancin PDP
Manyan Labarai

Yadda Gwamnatin Tarayya Ta Dakile Yaɗuwar Ɓarkewar Cutar Dabbobi A Jihar Jigawa

November 1, 2025
Jerin Gwarazan Taurarinmu
Manyan Labarai

Jerin Gwarazan Taurarinmu

November 1, 2025
Donald Trump Zai Gurfana A Gaban Kotu Kan Tuhumar Da Ake Masa
Manyan Labarai

Trump Ya Ayyana Nijeriya A Matsayin Ƙasar Da Rayuwar Kiristoci Ke Cikin Hatsari

October 31, 2025
Next Post
Ko Jam’iyyun Adawa Na Iya Kai Bantensu A 2027?

Ko Jam’iyyun Adawa Na Iya Kai Bantensu A 2027?

LABARAI MASU NASABA

Musabbabin Hana Sule Lamido Fom Ɗin Takarar Shugabancin PDP

Yadda Gwamnatin Tarayya Ta Dakile Yaɗuwar Ɓarkewar Cutar Dabbobi A Jihar Jigawa

November 1, 2025
Jerin Gwarazan Taurarinmu

Jerin Gwarazan Taurarinmu

November 1, 2025
CMG Ta Kammala Gabatar Da Rahoto Kan Ganawar Shugabannin Sin Da Amurka

CMG Ta Kammala Gabatar Da Rahoto Kan Ganawar Shugabannin Sin Da Amurka

October 31, 2025
Ministan Wajen Malawi: Tsarin Ci Gaban Kasar Sin Ya Samar Da Darussa Ga Kasashe Masu Tasowa

Ministan Wajen Malawi: Tsarin Ci Gaban Kasar Sin Ya Samar Da Darussa Ga Kasashe Masu Tasowa

October 31, 2025
Xi: A Shirye Sin Take Ta Hada Hannu Da Canada Wajen Mayar Da Dangantakarsu Bisa Turbar Da Ta Dace

Xi: A Shirye Sin Take Ta Hada Hannu Da Canada Wajen Mayar Da Dangantakarsu Bisa Turbar Da Ta Dace

October 31, 2025
Donald Trump Zai Gurfana A Gaban Kotu Kan Tuhumar Da Ake Masa

Trump Ya Ayyana Nijeriya A Matsayin Ƙasar Da Rayuwar Kiristoci Ke Cikin Hatsari

October 31, 2025
Yadda Waliyin Amarya Ya Sace Sadaki A Kano

An Tsare Wani Mutum A Gidan Yari Kan Zargin Kashe Matarsa Saboda Ƙuli-Ƙuli A Kano

October 31, 2025
Xi Ya Gabatar Da Rubutaccen Jawabi Ga Taron Kolin Shugabannin Masana’antu Da Kasuwanci Na APEC

Xi Ya Gabatar Da Rubutaccen Jawabi Ga Taron Kolin Shugabannin Masana’antu Da Kasuwanci Na APEC

October 31, 2025
Gwamna Uba Sani Ya Gabatar Da Kudirorin Raya Jihar Kaduna A Taron Ƙoli Na Biranen Asiya A Dubai 

Gwamna Uba Sani Ya Gabatar Da Kudirorin Raya Jihar Kaduna A Taron Ƙoli Na Biranen Asiya A Dubai 

October 31, 2025
Ya Kamata Sin Da Amurka Su Zama Kawayen Juna Ba Abokan Gaba Ba

Ya Kamata Sin Da Amurka Su Zama Kawayen Juna Ba Abokan Gaba Ba

October 31, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.