Daga Abubakar Abba
Fadar Shugaban ƙasa ta fitar da takarda akan cikar Nijeriya shekaru 57 da samun ’yancin kai, inda ta zayyana ɗimbin nasarorin da aka samar a ƙarƙashin mulkin Shugaba Muhammadu Buhari.
Takardar wadda ta fito daga Ofishin Mataimakin Shugaban Ƙasa, Farfesa Yemi Osinbajo ta zayyana nasarorin akan fannoni daban-daban, waɗanda suka haɗa da; harkar tsaro da tattalin arzikin ƙasa, yaƙi da cin hanci da rashawa da sauransu.
Takardar ta ce, harkar tsaro ita ce kan gaba a cikin jerin nasarorin da gwamnatin Buhari ta samar tun ɗarewarsa karagar mulki, cikin shekaru biyu da suka gabata.
Sauran nasarorin ƙarƙashin harkar tsaro sun haɗa da; magance rashin tsaro da daƙile ayyukan ‘yan Boko Haram a yankin Yamma Maso Kudu a ƙananan hukumomi 14 da suka mamaye da kuma sake gina rayuwar ‘yan yankin kimanin miliyan ɗaya waɗanda yaƙin ya ɗaiɗaita, waɗanda kuma tuni wasu sun koma yankunan su.
Fadar ta kuma zayyana nasarar da ta samu wajen magance masu yin garkuwa da mutane a ɗaukacin faɗin ƙasar nan, haɗe da cafko gaggan iyayen gidan masu aikata garkuwa da mutane da fasa inda suke ɓoye mutane in sun yi garkuwa da su a ɗaukacin faɗin ƙasar.
Gwamnatin ta kuma dawo da martabar Sojoji, inda aka wadata su da makamai, ta hanyar sawo masu jiragen yaƙi guda 12 masu suna ‘Super-Tucano’ akan kuɗi Dalar Amurka miliyan 600 don taimaka wa aikin su a Yamma Maso Kudu da kuma ci gaba da tabbatar da zaman lafiya
a yankin Neja Delta da kuma ci gaba da tura kuɗaɗe a shirin gwamnatin tarayya na afuwa ga tsagerun ‘yankin.
Gwamnatin ta kuma ce ta samu nasara wajen ƙirƙirar; bayar da tallafi na kaitsaye ga ‘yan gudun hijira da yaƙin Yamma Maso Gabas da yaƙin Boko Haram ya ɗaiɗaita, ƙarƙashin shirinta na musamman.
A kan harkar tattalin arzikin ƙasa kuwa, takardar ta zayyana nasarorin da ta samu waɗanda suka haɗa da; ƙaddamar da maido da tattalin arzikin ƙasa da kuma tsamo taɓarwarewar tattalin arzikin ƙasa data tsinci kanta a shekaru 29 duk da arzkin da aka samu ta hanyar Man fetur.
Ta bayyana cewar, an kashe Naira tiriliyan 1.2 wajen samar da ababen more rayuwa akan ayyukan da aka gudanar a ɗaukacin faɗin ƙasar nan, inda ta bayyana cewar, wannan ɗimbin nasara ce a bisa tarihin ƙasar nan.
Gwamnatin ta buga misali da ƙaddamar da tsarin lambar Banki ta BƁN, wanda ta ce, ta yi ne da nufin daƙile cin hanci da rashawa da rufe hanyar karkatar da kuɗin gwamnati ta hanyar ƙirƙirar Asusun bogi a Bankuna.
Don samar da sauƙi wajen gudanar da harkar kasuwanci kuwa, gwamnatin ta rattaba hannu akan dokar ƙudirin Majalisar ƙasar don bada damar gudanar da cinikayya ta shekarar 2017, ta bada damar samar da bashi ga ‘yan ƙasa cikin sauƙi, musamman wajen inganta kayan da ake
sarrafawa a cikin ƙasa.
Kafa zauren tuntuɓa da ke ƙarkashin fadar Gwamnatin Tarayya na gudanar da harkar kasuwanci a duk tsakiyar shekara, wanda ake tattaunawa da kamfanoni masu zaman kansu don bunƙasa tattalin arzikin ƙasa da kuma mayar da cibiyoyin gwamnatin kan tsarin gudanar da aikin gwamnati ta hanyar ‘E-goɓernance’ da kuma ƙirƙiro da gidauniyar yin amfani da na’urar zamani don ciyar da tattalin arzikin ƙasa gaba.
Akan yaƙi da cin hanci da rashawan dai, gwamnatin ta bayyana cewar, an samu nasarar hukunta jami’an gwamnati da ake zargi da hannu dumu-dumu wajen cin hanci da rashawa kuma an samu nasarori wajen ƙwato ɗimbin biliyoyin nairori na gwamnati da aka sace.
Gwamnatin ta ce, ta samu nasara wajen kafa tsarinta na busa Wusir da kuma sanya hannu akan Dokar gwamnati ta ‘004’ ta faɗar abin da jami’an gwamanti suke samu da kayan da suka mallaka, wanda an ƙirƙiro da dokar ce don wayar da kai da amince wa ƙara samar da kuɗin haraji da magance masu kaucewa biyan haraji.
An kuma samu nasara wajen rattaba hannu tsakanin Nijeriya da wasu ƙasashen duniya, don samar da hanyar samar da bayanai a zamanance da kuma rattaba hannu tsakanin daulolin ƙasashen larabawa maido da kuɗaɗen da wasu suka sace na gwamnati zuwa gida Nijeriya, inda an yi hakan ne, don ƙara inganta gangamin yaƙi da cin hanci da rashawa a Nijeriya.
Gwamnatin ta ce, ta kuma ƙirƙiri ‘PACAC’ don samarwa da shugabancin ƙasar nan alƙibla mai ɗore wa da kuma ƙarfafa jami’an gwamnati wajen yaƙi da cin hanci da rashawa.
Bugu da ƙari, gwamnatin ta bayyana cewar ta samu nasara wajen yaƙar cutar Foliyo da kuma ƙirƙiro da cibiyoyin matakan lafiya na farko a kowacce mazaɓa da ke ƙasar nan.