Gwamnatin tarayyar Nijeriya, ta biya ragowar bashin da kam-fanin sufurin jiragen sama na tarayyar Turai ke bin ta, kimanin dalar Amurka miliyan 850.
Wannan jawabi, ya fito ne daga bakin Jakadiyar Tarayyar Turai a Nijeriya da kuma Kungiyar Raya Kasashen Afirka ta Yamma (ECOWAS), Samuela Isopi, a yayin taron bunkasa kasuwanci tsakanin Nijeriya da Kungiyar Kasashen Turai (EU), karo na tara; wanda aka gudanar a babban birnin tarayya Abuja, ranar Talatar da ta gabata.
- CAF 2025: Nijeriya Ta Fito A Rukuni Mai Zafi
- Peng Liyuan Ta Yi Kira Da Karin Hadin Gwiwa Tsakanin Kasa Da Kasa Domin Takaita Cututtukan Kanjamau Da Tarin Fuka
“Har yanzu, Nijeriya ce kan gaba cikin jerin kawayen kasu-wancin Kungiyar Kasashen Turai (EU), a shekarar da ta gabata; domin kuwa, tana da alakar cinikayya wadda ta kai kimanin Yuro biliyan 35.
”Nijeriya, ita ce kasa babba wadda ke zuba jari a kasuwar Tarayyar Turai, domin kuwa tana da hannayen jari wadanda aka kiyasta cewa, za su iya kai wa kimanin Yuro bilyan 26, wan-da ya yi daidai da kwatancin kashi daya bisa uku na yawan jarin Nijeriya da ke can kasashen ketare”, in ji Isopi.
Har ila yau ta kara da cewa, akwai kamfanonin Tarayyar Turai sama da 230 da suke yin aiki a Nijeriya tare da samar da gura-ben aikin yi ga musamman matasa da kuma mata a fadin kasar.