Nijeriya Ta Fita Daga Kangin Koma-bayan Tattalin Arziki

Tattalin arziki

Daga Abdulrazaq Yahuza Jere,

Nijeriya ta yi nasarar fita daga kangin koma-bayan tattalin arzikin da ta tsinci kanta a ciki a karshen shekarar 2021, yayin da ta samu ci gaba da kashi digo shadaya a cikin dari (0.11).

Ci gaban da kasar ta samu a tattalin arziki yana nuna bunkasar da ta samu ne a sulusin shekara a karon farko idan aka yi la’akari da sulusin shekara guda uku da suka gabata.

Kamar yadda bayanan Hukumar Kididdiga ta Kasa suka nuna a ranar Alhamis, a yayin da sulusin shekara na hudu a shekarar 2020 ya nuna koma-baya a irin wanda aka samu a takwaransa na shekarar 2019 – da kashi 2.44 a cikin dari, an samu kari da kashi 3.74 a cikin dari idan aka kwatanta da sulusi na uku na shekarar 2020.

Fashin bakin da aka yi kan lamarin ya nuna an samu ci gaba bayan koma-bayan da aka samu a sulusi guda biyu na shekarar 2020.

“Kodayake ci gaban ba na a-zo-a-gani ba ne, amma dai yana nuna yadda hada-hadar tattalin arziki ke samun habaka sannu a hankali sakamakon sassauta dokar kulle da dabaibaye harkokin kasuwanci na cikin kasa da kasashen waje da aka samu a sulusan shekarar da suka gabata.” In ji rahoton.

Har ila yau, rahoton ya nuna cewa, burin da aka so ya cika a shekarar 2020 shi ne na samun ci gaba da kashi 1.92 amma kash! Sai aka samu koma-baya da kashi 4.20, idan aka kwatanta da abin da aka samu a shekarar 2019.

Hankulan masu tayar da tsigar jiki sakamakon koma-bayan tattalin arzikin da aka ce Nijeriya ta fada wa dai za su kwanta a halin yanzu saboda wannan kyakkyawan albishir da Hukumar NBS ta yi.

Exit mobile version